✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 5,000

Akalla Falasdinawa 5,140 ne Isra'ila ta kashe a Zirin Gaza, cikinsu har da mutum sama da 100 da ta kashe a daren Talata

Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 110 a daren Talata a Zirin Gaza, inda kawo yanzu yawan mutanen da ta kashe ya kai 5,140.

Kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza ta ce mutane 140 ne jiragen Isra’ila suka kashe a daren Talata, suka kuma kai hari a sansanin ’yan gudun hijira na Jabalia da ke Arewacin Gaza da kuma kusa da sansanin Nuseirat da ke tsakiyar yankin.

Gidan Talabijin na Al Aqsa ya ce Isra’ila ta kashe mutane 57 tare da jikkata wasu da dama a haren-haren da ta kai a kan gidaje a yankunan Rafah da kuma Khan Younis da ke Kudancin Gaza.

Akasarin wadanda Isra’ilar ta kashe kananan yara ne da mata a kwana 18 da ta shafe tana luguden wuta a Zirin Gaza.

Isra’ila kaddamar da haren-haren jiragen ne da sunan ramuwar gayya kan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga wata inda kungiyar ta kashe mutum 1,400, ta yi garkuwa da wasu daruruwa.

Hukumar Lafiya ta Zirin Gaza ta ce nan da sa’o’i 48 masu zuwa man da janaretocin wutar lantarki da ke asibitocin yankin zai kare.

A ranar Litinin ma’aiakatar ta sanar cewa asibitoci 32 sun daina aiki saboda hare-haren Isra’ila.

Tun ranar 9 ga wata Isra’ila ta hana shigar da mai da kayan abinci da sauran bukatu Zirin Gaza, ta kuma yanke wa yankin wutar lantarki da ruwan sha, ta hana mazauna fita zuwa wani waje.

Kakakin ma’aikatar lafiyar Gaza, Ashraf Al-Qudra ya sanar da cewa tsarin da aka yi na shigar da kayan agaji Zirin Gaza na tafiyar hawainiya, kuma ba za su yi tasirin a zo a gani ba.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya ce halin da ake ciki a Gaza na bukatar manyan motoci 100 a kullum.

Sai dai kawo yanzu, yawan motocin da suka shigar da kayan agaji yankin ba su kai 100 ba, tun daga ranar Asabar da suka fara samn izinin hukumomin kasar masar ta iyakar Rafah.