✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yadda muka rasa ’yan uwanmu 24 a hadarin mota’

A ranar Alhamis din makon jiya ne wani hadarin mota a Jihar Bauchi ya ci rayukan ’yan uwa ’yan asalin Jihar Katsina su 24 a lokaci…

A ranar Alhamis din makon jiya ne wani hadarin mota a Jihar Bauchi ya ci rayukan ’yan uwa ’yan asalin Jihar Katsina su 24 a lokaci guda.

“Har abada ba zan manta da wannan rana ta Alhamis 12 ga Disamban 2019 ba, ranar da aka yi jana’izar ’yan uwana mutum  24. Uku daga cikinsu ne ake iya ganewa ta hanyar ganin sauran jikinsu na zahiri, sauran 21 sai dai toka muka rufe domin sun kone kurmus.”

Wadannan su ne kalaman da suka fito daga bakin Alhaji Abdullahi Izma Yamadi, dan jarida da ke aiki a Gidan Talabijin na Jihar Katsina kuma Sakataren Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa reshen Arewa maso Yamma, lokacin da Aminiya ta tuntube shi kan wannan rashi na ’yan uwansa da suka yi a sanadiyyar wannan hadari da ya rutsa da su.

Shi dai wannan mummunan hadarin ya auku ne a kusa da garin Gubi  a hanyar Ningi zuwa  Bauchi, kuma wadanda suka rasu  suna hanyarsu ta zuwa kai amarya daga garin Dutsinma a Jihar Katsina, zuwa Yola sannan za su dauro auren wata amaryar daga can su dauko ta don kawo ta Dutsinma.

Kamar yadda Izma ya bayyana wa Aminiya, “Wadannan ’yan uwa namu sun fito ne daga rugage uku, Rugar Jan Gauta da Dogon Zoo da ta Katanga da ke Karamar Hukumar Dutsinma. Ka san yadda hidimar Fulani take in ta taso, kowane sashe na ’yan uwa sai an samu wakilci. To ba ma kamar wannan wanda muka bada kuma aka ba mu,” inji shi cikin hawaye.

Ya ce, “Jin wannan mummunan labari ya girgiza ni matuka, wanda ban tsaya wata-wata ba na tafi wajen da abin ya faru. Na gaza jure wa abin da idanuna suka gane mini. Akwai mata biyu da yara uku daga cikin wadanda suka rasu kuma aka gaza gane su saboda duk sun zama toka. Dukkansu 21 a cikin kabari daya aka rufe su domin ba a iya gane gawar namiji ko mace hatta ta yaran. Sauran wadanda aka ga namansu da za a iya cewa wannan na mutum ne, mun rufe na mutun uku.”

Su dai wadannan rugage uku da abin ya shafa, duk wanda ya shige su lallai ba a ce masa komai ba ya san akwai wani al’amari mai girma da ya faru na jimami.

Malama Yalli matar Malam Rufa’i daya daga cikin magidantan da suka rasu a hadari, wadda ya bar ta da ’ya’ya takwas, ta gaza yin magana da wakilinmu saboda bakin ciki sai dai nuni ta yi da hannu na alamun ba za ta iya magana ba, lokacin da muka tuntube ta.

Ta nuna da hannu cewa, shi ke nan mijinta ya tafi ba za ta kara ganinsa ba, inda alama ke nuna kamar ba ta cikin hayyacinta saboda kaduwa.

Malam Musa, ya rasa wansa, yayin da Malam Muntari ya rasa kanensa. Dukkansu sun ce babu abin da za su ce sai addu’ar nema wa ’yan uwansu gafarar Allah  musamman irin yadda Ya karbi kayansa ta hanyar konewa a wuta.

Sun ce in baya ga wadannan yara uku da mata biyu sauran duk magidanta ne wadanda shekarunsu suka fara daga 40 zuwa sama. Kuma babu wanda ba ya da iyali da ’ya’ya.

Aminiya ta samu bayanin cewa daga cikin yaran da suka rasa mahaifansu akwai masu karatun boko da ake fargabar da wuya su ci gaba da karatu ganin iyayensu da suka rasu ba masu karfi ba ne, ga kuma yanayin zaman ruga.

Wani wanda bai bayyana sunanasa ba ya shaida wa Aminiya cewa, akwai tsoron wadansu daga nan sun shiga halin kunci.

Bara’atu da Asubi ’yar Abdu Izma, matan Alhaji Abdu Buwa ne wanda ya rasu ya bar su da ’ya’ya 17 da sauran ’yan uwa.

Matan sun ce, su ko kuka ba su iya ba, saboda bakin ciki. Suka ce suna nema wa mijin gafara. Sun kuma ce, zai yi wuya su manta da shi a rayuwarsu irin yadda yake kyautata musu.

Sanusi shi ne babban dan Alhaji Abdu, ya ce, tabbas yanzu nauyi ya koma kansa kasancewarsa babba a wajen mahaifinsu. “Lallai muna cikin bakin ciki na rashin mahaifinmu da sauran dangi. Amma babu yadda za mu yi saboda haka Allah Ya hukunta. Can ne kasarsu take. Muna yi musu addu’ar Allah Ya gafarta musu,” inji shi.

Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa Mista Boboyi Oyeyemi wanda Kwamandan Hukumar ta Jihar Katsina Aliyu Sule Tanimu ya wakilta, ya mika ta’aziyya ga al’ummar yankin.

Da yake mika wa ’Yan Dakan Katsina Hakimin Dutsinma Alhaji Sada Muhammad Sada sakon ta’aziya, Shugaban Hukumar cewa ya yi, wannan ba karamin rashi ba ne ga karamar hukumar da Jihar Katsina da kasa baki daya bisa lura cewa, al’umma ce guda aka rasa a cikin wani irin yanayi.

Shugaban ya kara yin kira ga jama’a musamman direbobi su rika kiyaye doka yayin tuki.

Har zuwa rubuta wannan rahoto jama’a na ci gaba da zuwa ta’aziyya ga jama’ar yankin kan rasa ’yan uwa 24 a lokaci guda, ciki har da amarya.