A makon jiya da kuma wannan makon, jihohin Borno da Kano sun hadu da hare-haren da ake alakantawa da Boko Haram, inda a Borno aka ce sun yi kwanton bauna ga ’yan bangar da ke farautarsu. A Kano kuma bama-bamai suka dana a wuri biyu a yankin Sabon Gari, kuma mutane da dama sun rasu a hare-haren. Wakilanmu sun bi diddigin yadda lamarin ya kasance tare da tattaunawa da wadanda suka tsira daga hare-haren:
A ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe tara na dare ne lokacin da wasu ke Sallar Asham wasu bama-bamai suka tashi a kusan lokaci guda aTitin New Road kusa da Dandalin Ado Bayero da kuma Titin Enugu daf da Titin Ibo, abin da ya haifar da rudani a tsakanin jama’ar yankin, suka shiga guje-gujen neman mafaka.
Rabon da bam ya tashi a birnin Kano, tun a watan Maris da ya gabata inda fashewar wasu bama-bamai a tashar mota da ke Titin New Road a Sabon Gari ta halaka mutane da dama tare da jikkata wasu.
daya daga cikin mutanen da Aminiya ta tarar a wurin da bam din ya fashe a Titin New Road, Mista James Taiwo, ya ce labarin da ya ji shi ne mutanen da suka rasu sun kai 30. Mista Taiwo ya yi kira ga hukumomi su wayar da kan jama’a a kan su rika bin hanyar da ta dace wajen hana barna. Ya ce “Ko a cikin addinin Kirista shan giya haram ne, amma za ka tarar mutane suna shan ta. Abin da ya kamata a yi musu a nan shi ne a yi musu wa’azi ta hanyar lumana, ba ta irin wannan hanyar tayar da hankali ba.”
Ya ce amma yanzu haka wadanda ba mashayan ba ne, abin ya same su, don wasu suna harkar kasuwancinsu ne, wasu na wucewa, abin ya rutsa da su.
Shi kuwa Fidelis Machael da wakilinmu ya tarar a Asibitin Murtala wurin wata ’yar uwarsa da ta samu rauni, ya ce mutanen da suka rasu sun kai 40 ko fiye. Ya ce an dana bam din ne daf da wata mashayar giya ta waje inda aka jera kujeru, kuma bam din ya hada da wani karamin coci a cikin gida. Machael ya bayyana lamarin da abin tashin hankali, sai ya yi kira ga gwamnati ta tsaurara matakan tsaro.
Wata Misis Nkiru Sylbanus cewa ta yi “Bayan na fito tare da wata kawata da ta kawo min ziyara, na rakata ta hau babur mai kafa uku, ina kan hanyata ta komawa gida, sai kawai na ji wata kara mai karfi, mutane suka kama gudu. Iyakar abin da na sani ke nan ban ga yawan mutane da suka rasu ko suka ji rauni ba.”
A wuri na biyu da bam din ya fashe a Titin Enugu, ya lalata wasu motoci Golf da Marsandi. Wani mai suna Muhammad Abubakar ya shaida wa wakilinmu cewa harin bam din ba kunar bakin wake ba ne. Ya ce an dana bam din ne daf da wasu tebura na wasan kwallon sunuka. Ya ce ya samu labarin cewa mutum shida ne suka rasu, wasu goma kuma suka samu raunuka a tashin bam din na Titin Enugu kadai.
A Asibitin Murtala, wakilinmu ya tarar da wata mace mai suna Shade Durotade wadda ta ce ’yarta Deborah ’yar shekara tara, ta samu rauni a kafarta, a yayin fashewar bam din na titin New Road: “Muna zaune da dare sai na ji kara mai tayar da hankali, daga nan ne sai na ji Deborah ta yi kara, ashe burbushin bam ne ya same ta,” Shi kuma wani Mista Rotimi Kola ya ce ya kai ziyara ne ga surukarsa ’yar kimanin shekara 60, Mama Jomoke wacce ta samu rauni a sakamakon fashewar bam din.
kokarin da wakilinmu ya yi na shiga dakin jinya na “C” don tabbatar da yawan wadanda abin ya shafa, bai yi nasara ba, inda aka ce sai da izinin Babban Daraktan Lafiya, wanda ba ya nan, kuma mataimakinsa ya ce ba zai ba da izini ba, sai da izini daga shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci wadanda suka samu raunuka a Asibitocin Murtala da na Malam Aminu Kano, inda ya jajanta musu, ya ce, gwamnati za ta umarci jami’an tsaro su binciko wadanda suka haddasa wannan abin, kuma za a kara daukar tsauraran matakan tsaro don kauce wa faruwar hakan a nan gaba.
Kakakin Rundunar JTF a Jihar Kano Kyaftin Ikedichi Iweha ya tabbatar da faruwar lamarin, haka takwararsa na Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Magaji Musa Majiya, dukkaninsu sun ce ana ci gaba da bincike, kafin a tabbatar da yawan asarar da ta auku a tashin bama-baman.
Daga Maiduguri wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun yi dirar mikiya a garin Mainok da ke karamar Hukumar Kaga da kuma Dawashi da ke karamar Hukumar Kukawa a kusa da Tafkin Chadi a Jihar Barno inda suka halaka sama da mutum 40 a ranar Juma’a da Asabar din makon jiya.
Shaidu sun ce ’yan Boko Haram sun kona ’yan banga masu farautarsu (Cibilian JTF) hudu kurmus a garin Mainok. Kuma a lokacin da ake jana’izarsu ne matasa suka cafke wasu ’yan Boko Haram suka halaka biyu kuma suka tafi da daya.
An danganta hare-haren na Mainok da Dawashi da ‘daukar fansar’ da ’yan Boko Haram suka yi alkawari a kan matasa ’yan banga da ke Maiduguri wadanda suka sha alwashin farautar wakilansu. Yunkurin da samari da ’yan mata suke yi a Maiduguri ya sa yawancin ‘yan Boko Haram sun kaura zuwa kauyukan jihar da jihohin Yobe da Bauchi da Kano da Kaduna da wasu jihohi a Yamma da Kudancin Najeriya.
Bayan matasan sun kame da dama daga cikinsu, inda suka mika wasu ga jami’an Rundunar JTF, tare da halaka wasu da duka, ko yi musu wanka da fetur ana cinna musu wuta.
Bayanai sun ce matasan sun yi nasarar kamo ’yan bindiga da dama a garuruwan Bama da Dikwa da Gamborun Ngala da wuraren da ake ganin suna da sansani, bayan barin su Maiduguri. Sai dai farautar tasu ta tarar da cikas a makon jiya inda a Mainok akalla mutum 25 ne ’yan Boko Haram suka halaka, ciki har da ’yan Cibilian JTF hudu. Bayan ’yan Cibilian JTF sun kai samame Mainok sun cafke wasu ’yan Boko Haram, inda su kuma suka tare su a hanyar komawa Maiduguri suka bindige hudu daga cikinsu kuma suka cinna wa motarsu wuta.
Yawancin ’yan bangar suna amfani ne da itatuwa da sanduna da wukake da adduna da barandami da gariyo, kuma rashin kayan aiki kan saka su cikin matsaloli.
Bayanai sun tabbatar da cewa, bayan ’yan Boko Haram sun halaka ’yan Cibilian JTF a Mainok, sun kuma yi mummunar rauni ga wasu da dama inda aka kai su Asibitin Umaru Shehu da ke Maiduguri.
Shugaban ’yan bangar Maiduguri Abubakar Malum ya bayyana wa Aminiya cewa akalla yaransa uku ne suka rasu a asibiti, wasu da dama kuma suna jinyar raunukan da suka samu.
Wani dan banga da ke farautar ’yan Boko Haram Malam Mustapha Ibrahim ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da daddare bayan an gama farautar ’yan Boko Haram. “Su Cibilian JTF sun zo Mainok ne da motocinsu kirar Golf guda biyu da kuma bas kirar Model F, daya. Bayan sun kammala binciken da za su yi ne suna hanyarsu ta komawa Maiduguri sai ’yan bindiga suka tsare su. Motocin Golf din biyu sun wuce ke nan sai ’yan bindigar suka bude wa bas din wuta. Nan take motar ta tsaya kuma ’yan bindigar suka banka mata wuta,” inji shi.
Ya ce akalla sun kirga gawarwaki hudu da suka kone kurmus, sai daya da bai kone ba, amma ya mutu saboda harbin da aka yi masa da bindiga.
“Muna so gwamnati ta tallafa mana wajen hada mu da sojoji muna tafiya tare da su wajen yin farautar da muke yi,” inji shi.
Shi ma Muhammadu Bakoro wanda dan bangar da ke farautar ’yan Boko Haram ne ya ce abin da suke yi jihadi ne domin su kwaci kanmu. “Bayan muna yin bincike sai wasu munafukai suka sulale daga cikin gari suka je suka yi kwanton bauna a bayan gari suka auka wa yaranmu da ke komawa Maiduguri. Akalla yara biyar suka halaka,” inji shi.
Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka ta shigo cikin hidimar yadda ya kamata domin a share musu hawaye daga masifar da ke damunsu. Ya ce sun yi nasarar kashe ’yan bindiga biyu sun kama daya, kuma ya shaida musu akwai bindigogi a Mainok za su je su bincika.
Rundunar Hadin Gwiwa ta Najeriya da Kamaru da Nijar (MNJTF) mai matsuguni a Kukawa ta tabbatar da mutuwar mutane a garin Dawashi, inda ta ce lamarin ya auku ne lokacin da ’yan Boko Haram suka bude wuta ga ’yan bangar da suka je don farautarsu. “Ganau a garin da suka nemi a boye sunansu sun ce, “Wani rukunin ’yan banga sun isa garin Dawashi don zakulo ’yan Boko Haram inda su kuma suka bude wuta suka halaka farar hula fiye da 20 tare da raunata da dama,” inji Kakakin MNJTF Laftana Haruna Sani cikin wata sanarwa da ya aika wa manema labarai ta intanet.
Ya ce, “Wadanda aka halakan galibi masunta ne da ’yan kasuwa da ke yankin. Kuma tuni aka tura karin sojoji daga MNJTF domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiya a yankin. Galibin yankin Dawashi da Daban Masara da kuma Malan Karanti sanannu mazauni na wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne.”