Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kuɗi ga iyalan ’yan banga da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki.
Kuɗaɗen wanda Daraktan ayyuka na musamman, Muhammad Alhaji Baba ya miƙa a madadin sakataren gwamnatin jihar sakamakon umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bayar na a yi hakan.
Wannan shiri dai wani ɓangare ne na shirin jin daɗin jama’a na jaha ga jami’an tsaro domin tabbatar da cewa, iyalan ’yan banga da abin ya shafa sun samu tallafi.
A ƙarƙashin shirin, kowane dangin ɗan banga da ya rasu ya karɓi Naira dubu ɗari ₦500, yayin da waɗanda suka jikkata an ba su Naira dubu ɗari ₦200 kowanne.
Da yake jawabi a lokacin rabon kuɗaɗen, Daraktan ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da suka haɗa da ƙungiyoyin ‘yan banga domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a Jihar Yobe.
Ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma yaba da jajircewa, sadaukarwa da ‘yan bangar suka yi wajen tabbatar da tsaron jihar.
“Jarumtar da kuke nunawa lalle kuna yinta bisa ƙa’Ida, kuma jin daɗin ku ya kasance babban fifiko ga wannan gwamnati,” in ji shi.
Tallafin kuɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin tsaron al’umma da kuma ba da agaji ga waɗanda abin ya shafa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya.”