Muhammad Nura wanda aka fi sani da Dandolo dan wasan barkwanci ne a masana’antar Fina-Finan Hausa ta Kannywood.
A wannan tattaunawa, ya yi bayani kan rawar da yake takawa a shirin wasan ‘Gidan Badamasi’ da sauran batutuwa:
Yaya aka yi ka tsinci kanka a harkar wasan kwaikwayo?
Na fara harkar ce tun daga wata kungiyar wasan kwaikwayo a makarantar sakandarenmu a Giwa da ke Jihar Kaduna, inda abin ya ci gaba da zame mini jiki bayan tasowata.
Lokacin da na dawo mahaifata ta Samaru, Zariya, sai muka kafa wata kungiyar wasan kwaikwayon mai suna Gaskiya Youth Club, wacce daga bisani muka canja wa suna zuwa Gamzaki.
Har yanzu wannan kungiyar tana nan da ranta da mutane da dama a cikinta, yawancinsu matasa.
Daga bisani kuma na tafi garin Wudil a Jihar Kano domin daukar wasu wasanni.
Mu ne muka fara wasa a masana’antar fina-finan da a yau ake kira da Kannywood.
A lokacin mun fara ne da ’yan wasa kamar su marigayi Ibro da Kulu da Sadi Sidi Ishak da Danwanzan da sauransu.
Har yanzu ina iya tuna yadda a lokacin Alhaji Musa Na-Saleh zai bayar da Naira 1,000 mu yi wasan kwaikwayo har mu sallami kowa duk a ciki.
Gaskiya kusan zan iya cewa a garin Wudil masana’antar Kannywod ta fara kafin daga bisani ta kaura ta koma Kano.
Za ka kai shekaru nawa a masana’antar Kannywood?
Na kasance a masana’antar nan sama da shekara 30 kuma na fito a fina-finai sama da 200 zuwa yanzu.
Baya ga wasan kwaikwayo kana da wata sana’a?
Ni masunci ne kuma maginin gargajiya ne; Na gaji wadannan sana’o’in ne daga iyaye da kakanni.
Wadannan su ne sana’o’ina banda wasan kwaikwayo.
Duk lokacin da ba na shirin wasan kwaikwayo to alal hakika za ka same ni ko dai ina gini ko kuma sana’ar su.
Ka yi fice a cikin fina-finanka wajen kada kaca-kaura. Shin shi ma na daga cikin abubuwan da ka gada?
Sam, ko daya ba gada na yi ba, kawai dai an kalubalance ni ne da in koya kuma in rika yi.
Hakan ta faru ne lokacin da nake koyar da kidan ganga.
To akwai wani mutum da yake kada wannan kaca-kaurar ni kuma nakan bi shi kasuwanni inda yake zuwa don yin wasanni a can.
Kwatsam wata rana sai na dauka ni ma na fara jarrabawa. A lokacin ma sai da ya fusata har ya zazzage ni a kan wai me zai sa in dauka.
Daga nan ne ni kuma na kudiri aniyar koyon kada ta komai wuya.
Da na koma gida sai na hada nawa kuma sannu a hankali na fara kwarewa.
Na koma Kano na fara kadawa, kan ka ce kwabo na fara yin suna saboda irin shigar da nake yi da irin wakokin da nake rerawa yayin kadawar.
Bayan wasu ’yan watanni sai na koma wurin mutumin da ya taba zagi na a kanta.
Sai ake shaida masa cewa yanzu fa akwai wanda ya fi shi iya kadawa yana nan zaune a nan yankin.
Ya zo ya same ni, har kudi sai da ya ba ni. Ya manta cewa ni ne wanda ya taba zagi a kan lamarin.
Amma daga baya na koma na tuna masa labarina.
Me ya sa kake amfani da kayan sawa da suka sha bamban da na sauran jarumai a cikin wasanninka?
Duk wani mai wasan barkwanci da yake so ya darar wa sa’a dole ne ya kasance mai kirkira.
Na dauki rigar da ta fi kama da ta mata domin amfani da ita wajen wasan kwaikwayona.
Ina da sunan wasa daban-daban, kowannensu kuma ya danganta da irin rawar da zan taka a cikin shirin da zan fito.
Yaya za ka kwatanta salon rawar da kake takawa a cikin shirin Gidan Badamasi da wadanda ka yi a baya?
Yaya Dankwambo shi ne matsayin da nake fita a shirin Gidan Badamasi wanda a zango na biyu na shirin ya kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da suka taba faruwa ba wai gare ni kawai ba, a’a har ma da masana’antar Kannywood baki daya.
Shirin wasan kwaikwayo ne da yake nishadantarwa ya kuma fadakar.
Yana kuma samun dimbin masu kallo wadanda su ma ake ba su damar tofa albarkacin bakinsu a ciki.
Idan na koma kan tambayar da ka yi mini, abin da ya bambanta shi da ragowar shiryeshiryen, shi ne shi wannan wani shiri ne mai dogon zango da ake nuna wa mutane kuma yake nishadantarwa ya kuma ilimantar.
Saboda haka dukkan taurarin cikin shirin na kallon kansu kamar wadansu ’yan gida daya.
Wane lokaci ne ba za ka taba mantawa da shi ba a matsayinka na jarumin wasan kwaikwayo?
Lokacin da ya fi burge ni shi ne wanda na iya taka rawar da aka ba ni a cikin shiri yadda ya kamata kuma yadda ake bukata.
Ba na da-na-sanin kasancewata mai wasan kwaikwayo ko kadan’.