Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce duk da yadda ake ganin matsalar tsaro a Najeriya, akwai kashe-kashe da dama ba kafafen yada labarai ba su da labari.
Da yake jawabi a taron Majalisar Addini ta kasa a Abuja, Sarkin Musulmi ya ce duk da cewa matsalar tana raguwar, shi ba zai daina gaya wa gwamnati gaskiya ba.
- Mutanen kauyuka na sayen bindigogi don kare kai
- Abin Da Ya Sa Tashe-Tashen Hankula Suka Ki Karewa A Najeriya
“A Sakkwato kadai akwai ranar da muka binne mutum 76 da miyagu suka kashe haka kawai, amma mutane ba su da labari.
“Har wa yau a Sakkwaton, akwai wata rana da muka binne mutum 48, shi ma mutane ba su samu labari ba.
– A hukunta ko waye
“Dole a gano masu aikata wannan ta’asa, hukumomin tsaronmu su tashi shaikan su yi aikinsu, su gano wadannan mutane, a sauki mataki a kansu, ko da shugabannin addini ne ko shugaban kabilu ne.”
A cewar Sarkin Musulmi, “A cikin shugabannin siyasa da na addinai kuma akwai masu yin kalaman tsana; Amma ba yadda za ka kashe mutumin haka kawai ka shiga Aljanna, sai dai ka rudi kanka, wuta za ka shiga.
“Dole a gano duk mai yin irin wannan, sannan jami’an tsaro su dauki mataki a kansa ko wane ne shi.
“Ko basarake ne ko shugaban siyasa ko shugaban addini ko na kabila, dole ne a hukunta shi tunda ai babu wanda ya fi karfin doka,” inji shi.
– Kar a shigo da kasashe waje
Ya kuma yi gargadi cewa a guji gayyato kasashen waje kan wannan matsalar, “Dole mu tashi mu kawo karshen matsalar.
“Idan kuma aka yi sakaci aka bari kasashen waje su shigo su magance matsalar da muka kasa, to abin a zai biyo baya ba zai yi mana dadi ba.
“Ina magana ne da babbar murya domin mun damu matuka da irin abin da muke gani yana faruwa,” inji shi.
Game da maudu’in taron na wannan karo; “Samar wa ’yan Najeriya lafiya do zaman lafiyar a al’umma,” Sarkin Musulmin ya ce ya yi amannar cewar samar da zaman lafiya na bukatar tattaunawa ta gaskiya.