More Podcasts
’Yan Najeriya mazauna yankunan da ke iyakar kasar Jamhuriyar Nijar na dandana kudarsu sakamakon tsadar rayuwa da tashin gwauron zabon kayan masarufi, tun bayan rufe bodar da Najeriya ta yi a watan Agusta.
Anya wannan rufe boda da Kungiyar ECOWAS ta sa aka yi, ba za a ci kai da kai ba?
- ‘Dalilin Da Muke Shan Maganin Karfin Maza’
- Yadda Ba Wa Masu Shigo Da Shinkafar Waje Dala Zai Shafi Farashin Ta Gida
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya ziyarci garin Illela a Jihar Sakkwato da Maigatari a Jihar Jigawa, da kuma Kwangalam da Jibiya a Jihar Katsina, domin jin halin da mazauna garuruwan suka tsinci kansu a tsawon lokacin da ka rufe bodar, a matsayin garuruwan ma masu alakar kasuwanci da makwabtansu da ke Nijar.
Shirin na kuma dauke da fashin baki tare da wani masanin tattalin arziki a game da wannan al’amari.
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan