✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa

Gwamnatocin sojin Nijar da Mali da Burkina Faso sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyonsu na haɗin gwiwa ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje…

Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa.

Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu.

Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”

Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da kuma bankin saka hannun jari, wanda ya ƙara nuna jajircewarsu ga haɓaka haɗin kai da ci-gaba a tsakanin ƙasashe mambobin AES.

A watan Janairu na 2025 ne  ƙasashen uku da suka kafa ƙungiyar ta AES, suka sanar da ficewarsu a hukumance daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).

Makonni uku da suka gabata, ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin sojoji, sun ɗora harajin shigo da kaya na kashi 0.5 bisa ɗari a kan kayayyaki daga ƙasashen ECOWAS.

Harajin ya shafi duk kayayyakin da suka shigo daga ƙasashen ECOWAS zuwa kowace daga cikin ƙasashen uku, banda kayan agajin jin kai.

Wannan tsarin ya yi karo da shirin ECOWAS na tabbatar da zirga-zirgar kayayyaki a tsakanin mambobinta da ƙasashen AES duk da ficewarsu a hukumance daga ƙungiyar a watan Janairu.