✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matsalar ruwan sha ta addabi Kanawa

Mu dai bamu kara kudin ruwan ba, amma rashin wuta ya jawo ruwa yana wahala.

A yayin da yanayin zafi ya kankama, jama’a a Jihar Kano sun koka matuka kan yadda suke shan wahala wajen samun ruwan amfani na yau da kullum a ciki da fadin jihar.

Baya ga wahalar da ake sha wajen samun ruwan, jama’ar sun koka sakamakon tsadar da ruwan ya yi, inda a wasu sassan ake siyar da ruwan a kan kudi N70, sabanin N30 da ake siyarwa a baya.

A wani zagaye da jaridar Aminiya ta yi, ta gano cewar kusan kowacce unguwa a birnin Kano na fama da matsalar ruwa, musamman a wannan wata na Azumi da bukatar ruwan ta ke karuwa.

Da yawa daga cikin unguwannin sun dogara ne da ruwan da ake siyarwa a burtsatse daga hannun masu tallan ruwa a cikin jarkoki da aka fi sani da ’Yan Garuwa.

Unguwannin da suka fi fama da wananan matsala sun hada da yankin Kurna, Bachirawa, Fagge, Yakasai, Birged, Hotoro, da ma wasu sassan kwaryar birnin Kano.

Malam Abdullahi Adamu, mazaunin unguwar Hotoro ya bayyana wa wakilinmu cewa sama da shekaru 20 bai ga ruwan famfo a unguwar ba, inda kuma ya koka kan cewar farashin jarkar ruwa ya nunka da kaso 100 a unguwar tasu.

“Jarkar ruwa mai lita 25 wadda a da muke siya N20 yanzu ta koma N40, wani lokacin ma har N50. Satin da ya wuce ma sai da na sayi ruwa N70,” inji shi.

Wasu masu ga ruwa a Kano

Shi ma wani mazaunin unguwar Kurna mai suna Ya’u Zubairu, ya ce a kwanan baya sai da suka sayi jarkar ruwa akan kudi N100 sakamakon barazanar shiga yajin aiki da masu siyar da ruwan suka yi, wanda ya jefa su cikin bakar wahala.

Sai dai a nasu bangaren, su ma masu siyar da ruwan,  sun bayyana cewa farashin ruwan ya tashi da kusan kaso 100 na yadda suke siyowa a baya.

Wani mai siyar da ruwa a unguwar Kurna mai suna Sani Jibrin ya bayyana wa Aminiya cewar, “A da muna siyan jarka 12 a kan N150, amma yanzu ya koma N250.

“Wani lokacin ma yana kaiwa N300. Kaga ya zama dole mu ma mu kara kudi, idan ba haka ba babu riba. Sana’ar mu akwai wahala.”

Su ma masu gudanar da burtstate sun bayyana nasu dalilin na kara kudin ruwan, inda suka ce ya samo asali ne daga tsadar man disel.

“A kullum muna siyan diesel na N45,000 wanda da shi muke samar da ruwan. Don haka ya zama dole mu kara kudi in ba haka ba kuwa sai dai mu hakura, domin kuwa faduwa za muyi,” inji wani Aliyu Umar mai kula da tankin ruwa a Kurna.

Shi ma wani mai kula da famfon ruwa a Kofar Nasarawa ya ce su dai basu kara kudin ruwan ba, amma “rashin wuta ya jawo ruwa yana wahala.

“Mu muna amfani da famfo ne, kuma muna da kan famfo sama da 30 a nan, amma in dai babu wuta to ba ma aiki, kuma yanzu wuta bata samuwa sosai.”