✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matashi ke amfani da asiri wajen damfarar masu POS

Yakan yanka fararen takardu ya bayara a saka masa a banki

’Yan sanda a jihar Anambra sun cafke wani mai suna Chisom Nwekeda ya kware wajen yin amfani da asiri don damfarar masu sana’ar POS a Awka, babban birnin jihar da kewaye.

Matashin, mai kimanin shekara 26 ya shiga hannu ne ranar 15 ga watan Satumban 2022 a karamar hukumar Amawabia da ke jihar.

A cewar wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, Ikenga Tochukwu ya fitar ranar Alhamis, tuni wanda ake zargin ya amsa aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Ikenga ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa wanda ake zargin yakan yanka fararen takardu ne daidai dz tsayin takardun kudi sannan ya ba masu POS da nufin su saka masa a asusun ajiyarsa na banki.

Kakakin ya kuma ce yanzu haka rundunar na kokarin ganin yadda za ta kamo ragowar abokan damfarar Chisom din nan ba da jimawa ba.