Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami’an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ’yan kasar miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma’a.
Sanarwar ta ambato EFCCn tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu.
Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun.
Sauran sun waɗanda ta ce ’yan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno da Israel Mbaluka da Joseph Kabera da kuma Serah Michiro.
“Muna son sanar da al’umma cewa muna neman waɗannan mutane ruwa a-jallo saboda zargin damfarar mutane a wani tsarin zuba kuɗi na intanet wanda ake kira CBEX,” in ji EFCC.
Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa jami’an EFCC ɗin damar kame da kuma tsare mutanen da aka samu da hannu wajen yaɗa tsarin na CBEX.