Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya gwangwaje wata yarinya ’yar sakandire mai shekaru 15 da tallafin karatu saboda fasaharta ta zane-zane.
Yarinyar, mai suna Amina Abdullahi, wacce daliba ce a makarantar sakandiren Gobarau da ke Katsina dai ta sami tallafin ne yayin wani bajekolin fasaha da aka gudanar a ranar Asabar, inda gwamnan ya ce fasahar ta cancanci yabo.
Masari ya yi alkawarin cewa Jihar za ta dauki nauyin karatun nata ne har zuwa matakin jami’a, baya ga biya mata kudaden jarrabawar NECO da WAEC da kuma ta JAMB.
“Fasaha irin wannan na taimakawa kirkira da dogaro da kai, tana bukatar a karfafa mata gwiwa domin ta fito da ainihin baiwarta,” inji Gwamnan.
Daga nan sai yaba wa wadanda suka shirya bajekolin bisa kokarinsu na zakulo masu fasahar da za su taimaka wajen ci gaban Jihar da ma kasa baki daya.
A cewarsa, hakan zai taimaka wa dalibar da ma sauran masu fasaha irin nata su cimma burinsu na ciyar da al’umma gaba.
A nasa jawabin, shugaban masu shirya gasar ta Kastina Talent Hunt, Akitek Faisal Jafar yaba wa gwamnan ya yi kan irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban matasa a matsayinsu na manyan gobe.
Ya ce suna aiki ba dare ba rana wajen zakulo matasa masu fasaha a Jihar domin a tallafa musu su cimma burinsu. (NAN).