A ranakun Talata zuwa Juma’a na makon da ya gabata (3 zuwa 6-10-2017), marubuta da masana daga sassa daban-daban na kasar nan ne suka halarci gagarumin taron kara wa juna sani, wanda kungiyar Marubuta ta Najeriya, Reshen Jihar Katsina ta dauki nauyin gudanarwa.
Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Sakatariyar Jihar Katsina, mahalarta sun rika zuwa ne a kowace safiya, daga karfe 9:00 zuwa 6:00 na maraice, inda masana wato manyan malaman jami’a da marubuta suka gabatar da mukaloli kan bayanai daban-daban da suka shafi adabi.
Tun da farko dai, a jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar ta marubuta reshen Jihar Katsina, Muhammad Kabir Sani ya bayyana dalilin kungiyar na shirya wannan gagarumin taro, wanda ya ce shi ne irinsa na uku da marubutan suka shirya a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Kamar yadda ya ce, an fara gudanar da irin wannan taro ne a Jihar Neja, aka sake gudanar da karo na biyu a Jihar Kebbi, inda kuma a bana Jihar Katsina ta amshi bakuncin taron na bana. Ya bayyana cewa taron yana ba marubuta, musamman na Arewa dama su gana da juna, su kara wa juna sani kamar kuma yadda suke baje kolin fasaharsu da suka hada da gabatar da gajerun kirkirarrun labarai, wasannin kwaikwayo da rubutattun wakoki.
Shugaban, ya yi kira ga gwamnatoci, musamman Gwamnatin Jihar Katsina da ta ci gaba da tallafa wa marubuta, domin bunkasa shirinta na bunkasa ilimi a jihar da ma kasa baki daya. Ya bayyana cewa marubuta su ne kashin bayan ci gaban ilimi a cikin al’umma, don haka za su ci ngaba da aiki tukuru wajen fadakarwa, ilimantarwa da kuma nishadantarwa a cikin rubuce-rubucensu domin gina al’umma.
Shugaban taron ya kasance Sardaunan Katsina kuma Garkuwan Hausa, tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Alhaji Ibrahim Ahmadu Coomassie, sai dai bai samu halarta ta kansa ba, illa ya turo wakilcin kanensa, Alhaji dahiru Commassie.
A jawabinsa, a matsayinsa na shugaban taro, Sardauna Coomassie wanda kuma shi ne Shugaban kuungiyar Tutuba ta Arewa, ya yaba da taken taron na bana “Adabi Da Hadin Kan kasa: Gudunmowar Marubuta A Matsayinsu Na Jigon Gina kasa.” Ya ce wannan zai ba da dama a tattauana tare da gano matsalolin da ke kawo wa kasar nan cikas kuma a magance su.
“Idan muka lura, Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama tun samun ’yancin kai, shekaru 57 da suka gabata. Daga juyin mulkin soja na farko na ranar 15 ga Janairu, 1966, wanda ya kassara mulkin dimokuradiyyarmu na farko kuma ya haddasa kisan wasu daga cikin shugabanninmu masu mutunci, zuwa yakin basasa, wanda ya lakume rayukan miliyoyin ’yan Najeriya, kabilu sama da 300 suna ci gaba da rayuwa cikin dar-dar da juna. Wasu lokuta, wadannan rikice-rikicen kabilanci sun kaskantar da rayukan al’umma, sun lalata dukiya,” inji Alhaji Ibrahim Coomassie.
Ya yi kira ga membobin kungiyar Marubuta ta Najeriya da su karkata akalar rubuce-rubucensu wajen kawo hadin kai tsakanin al’ummar kasa, yadda za a samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummu daban-daban na kasar nan.
“Ba wai kawai za ku wanzar da hanyoyin hada kan juna ba ne da rubuce-rubucenku, za ma ku rika farfado da al’adar karatu, wacce kusan a ce ta mutu a Najeriya,” inji shi.
Taron ya ci gaba da gudana, inda Babban Mai Jawabi, Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina ya gabatar da nasa jawabin, wanda ya yi nazarin taken taron gaba daya. Masanin, ya yi bayani dalla-dalla, inda ya fayyace ma’anar manyan kalmomin da ke kunshe a taken taron, da suka hada da ‘Adabi,’ ‘Hadin Kan kasa,’ ‘Marubuta’ da sauransu.
Haka kuma, masanin ya yi nazarin yadda kalaman nuna kyama suka haddasa raba kan al’ ummar Najeriya, wanda haka ya haddasa rikice-rikice daban-daban a kasar kuma ya haifar da zullumi da gaba tsakanin mabambantan mutane da kabilu a Najeriya.
Da yake bayyana irin rawar da marubuta za su taka wajen kawo hadin kai ga kasa, kamar yadda taken taron ya nuna, Wazirin na Katsina ya bayyana cewa: “Marubuta za su iya taka gagarumar rawa wajen kasancewa tsani ko gada ta hanyar rubuce-rubucensu wajen hada kan al’ummar kasa, yadda Najeriya za ta zama dunkulalliyar kasa mai dauke da al’umma daya mai fahimtar juna. Haka kuma za su iya amfani da rubuce-rubucensu wajen raba kan al’umma wanda hakan zai haddasa wargajewar kasa.”
Don haka, ya kamata marubuta su jajirce, su zama masu rubutu mai ma’ana yadda za a gina kasa maimakon yin amfani da alkalaminsu wajen haddasa rigima tsakanin al’umma, wanda haka zai wargaza kasa.
A lokacin da aka zo wajen nishadantarwa, an gabatar da wasan kwaikwayo, kirari da kuma rubutattun wakoki ga mahalarta taron. Membobin kungiyar Marubuta Da Makaranta na Makarantar danmasani Academy sun gudanar da wani takaitaccen wasan kwaikwayo, wanda ke nuna muhimmancin hadin kai da fahimtar juna tsakanin kabilu daban-daban na Najeriya. Sarkin Fulani Dankama, Malam Ishaka ya gabatar da kirari daban-daban cikin azanci da balagar harshen Hausa. A yayin da Bashir Yahuza Malumfashi ya gabatar da wakokin fasaha guda uku bisa maudu’ai daban-daban da suka hada da: ‘Buhari Ikon Allah’ da ‘Kainuwa’ da kuma wakar Ingilishi mai taken ‘Sardauna.’
Kafin kammala bikin bude taron, Shugaban kungiyar Marubuta ta kasa (ANA), Denja Abdullahi ya yi kwarya-kwaryan jawabin yabawa da taron. Ya yi kira ga marubuta da su maida hankali wajen yin rubutu bisa la’akari da al’adunmu domin gyara tarbiyya da saita tunanin al’umma da nufin wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’umma. Ya jaddada muhimmancin da ke tattare da rubutu da marubuta wajen gina kasa da hadin kan al’umma. Bisa ga haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da gwamnatoci da su tallafa wa harkar rubutu da marubuta.
A lokacin da yake gabatar da nasa jawabin, a matsayinsa na Babban Bako, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, wanda Kwamishinan Watsa Labarai, Alhaji Hamza Muhammad Borodo ya wakilta, ya yaba da yunkurin kungiyar marubuta da ta shirya wannan gagaruin taro da nufin fadakar da al’umma muhimmancin rubutu da marubuta wajen hada kan al’umma. Ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshikin gina al’umma kuma shi ne tubalin samar da ci gaba a cikin al’umma.
“Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Dallatun Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ta dauki al’amarin ilimi da matukar muhimmanci a sahu na daya da na biyu da na uku. A shirye gwamnatin nan take ta yi duk abin da za ta yi wajen tallafa wa harkar ilimi. Haka kuma, kasancewar wannan kungiya ta marubuta da ta shirya wannan taro, burinta ne ta tallafa wa ilimi, babu shakka gwamnatin nan a shirye take ta hada kai da membobinta, domin bunkasa ilimi;” inji shi.
Kwamishinan, wanda ya wakilci gwamnna, ya ce zai sanar da Gwamna Masari irin bukatun kungiyar domin a ga yadda za a tallafa mata, domin ta ci gaba da ayyukanta na samar da ingantattun littattafan karatu don wayar da kan al’umma.
Wasu daga cikin abubuwan da aka gabatar a yayin taron, sun hada da kai ziyara ga muhimman mutane da kuma gidajen tarihi da ke birnin Katsina. Marubuta sun ziyarci fadar mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, wanda ya amshi tawagar marubutan cikin farin ciki.
A jawabinsa, sarkin na Katsina ya yaba da kokarin kungiyar, inda ya nemi lallai marubutan su maida hankali wajen rubuce-rubuce cikin harshen gida. Ya koka da yadda ya samu rahoton cewa an daina koyar da daliban firamare darussan Hausa da ilimin addinin Musulunci.
“Lokaci ya yi da za a maida hankali wajen bunkasa harshenmu na Hausa da kuma inganta al’adunmu na gargajiya. Idan ba mu yi haka ba, to har yanzu muna cikin kangin bauta. Idan mun lura, duk wata kasa da ta ci gaba, da harshen mutanensu suke gudanar da al’amura. A kasar Saudi Arebiya, Larabci ake yi, a kasar Jamus, da Jamusanci ake magana.” Inji sarkin na Katsina, wanda ya nemi kungiyar ta marubuta da ta dabbaka ayyukanta a aikace, kada ta tsaya shirya taruka kawai, a yi jawabai, a yi tafi a watse kawai ba.
Marubutan sun ziyarci hasumiyar Gobarau, masallacin da masana tarihi suka ce an gina shi sama da shekara 700 da ta gabata, kamar kuma yadda aka amince da cewa shi ne gini mai hawa sama da biyu da aka fara ginawa a daukacin nahiyar Afrika. An kuma ziyarci shahararrar makarantar Kwalejin Katsina, wacce ta yaye mafi yawa daga shugabanninArewa na farko, kamar su Sardauna Ahmadu Bello da Abubakar Imam da sauransu. Duk dai a lokaci daya kuma aka ziyarci Gidan Adana Kayan Tarihi na kasa, wanda ke dauke da kayayyakin tarihi dadaddu,
A yayin gudanar da taron, marubuta da fitattun malaman jami’a sun gabatar da takardu fiye da goma, wadanda suka shafi batutuwan adabi daban-daban. Wadanda suka gabatar da takardun sun hada da Malam Abdulwahid Usman na Jami’ar Alkalam Katsina da Dokta Wale Okediran da Malam Isyaku Bala Ibrahim na Cibiyar Kula Al’amuran Kamfanoni da kungiyoyi (CAC) Abuja da Farfesa Asabe Kabir ta Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato.
Sauran sun hada da Dokta Aliyu Ibrahim kankara na Jami’ar Tarayya Dutsin-ma da Farfesa Yusuf Adamu na Jami’ar Bayero Kano da Khalid Imam da danjuma Dogara Musa da Rukayya Mohammed Yunusa ta Jami’ar Alkalam Katsina da Hassan R. Kurfi na Kwalejin Kimiyya ta Hassan Usman Katsina da matashin manazarci, Saddik Dzukogi daga Jihar Neja da mahaifinsa, B, M. Dzukogi da sauransu.
Kafin rufe taron na kwana uku a daren Jumu’a, sai da aka gabatar da gagarumin bikin karrama wasu fitattun mutane da suka ko suke kan ba da gudunmowa wajen bunkasa ilimi a Najeriya. Wadanda aka karrama sun hada da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da Alhaji Umaru Dembo da marigayi Abubakar Imam da Dokta Yusuf Bala Usman da Mai Shari’a Musa danladi Abubakar da Malam Labo Yari da Hajiya A’isha Umar Muhammad da Dokta Bukar Usman da Hajiya Hafsat Abdulwahid da Dokta Halima Yalwa Adamu da Alhaji Bashir Tofa da marigayi Malam Hadi Alkanci.
Taron dai ya gudana cikin lumana, kamar yadda kuma aka kammala shi lami lafiya ba tare da wata matsala ba. A ranar Juma’a kuma mahalarta taron suka kama hanyar komawa gidajensu a sassa daban-daban na kasar nan, inda ake sa ran sake gudanar da taron kashi na hudu a wata jihar kuma ta Arewa nan gaba.