✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba

Gwamnan ya ce wannan dama ce da za a haɗa kan ƙasa da samar da tsarin shugabanci na gari.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dole ne, ya taimaka wajen haɗa kan ƙasa, kyautata mulki, da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya buƙaci a gudanar da wannan aiki cikin adalci, gaskiya da kuma bisa ra’ayoyin jama’a gaba ɗaya.

Gwamna Abba, ya bayyana haka ne ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sulaiman Wali.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da saƙon maraba da baƙi a wajen Taron Sauraron Ra’ayoyin Jama’a na Yankin Arewa maso Yamma kan sake gyaran kundin tsarin mulki, da aka gudanar a Kano ranar Asabar.

Yayin da yake maraba da kwamitin Majalisar Dattawa da sauran baƙi, gwamnan, ya ce wannan taro muhimmin mataki ne ga ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

“Yana da muhimmanci na tarbe ku zuwa Jihar Kano, mambobin kwamitin Majalisar Dattawa kan sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, domin wannan muhimmin aiki na ƙasa.

“Haka kuma muna maraba da ‘yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarta domin tattauna makomar ƙasarmu.

“Muna alfahari da cewa Kano, jiha mai yawan jama’a da tarihin siyasa, ce ke karɓar wannan gagarumin taro,” in ji shi.

Gwamnan, ya ce wannan taro na zuwa a lokacin da ya dace, kuma zai bai wa ‘yan Najeriya damar bayar da gudunmawa wajen tsara dokokin da za su tafiyar da ƙasar.

“Wannan taro yana nuna yadda muke jajircewa wajen ƙarfafa gwamnati mai nagarta da kuma gina ƙasa mai adalci da ƙwarewar shugabanci,” a cewarsa.

Ya bayyana kundin tsarin mulki a matsayin ginshiƙi da tushen kowace gwamnati.

“Kundin tsarin mulki shi ne zuciyar tsarin mulkin kowace ƙasa. Shi ne jagoran adalci da ginshiƙi a wajen jama’a.

“Shi ke ƙayyade dangantaka tsakanin gwamnati da jama’a. Saboda haka, dole a gudanar da sake gyaranss cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.

Gwamna Abba, ya kuma ne dole a tabbatar da cewa wannan sabon tsarin zai amfani kowa da kowa; daga Arewa zuwa Kudu, maza da mata, matasa da tsofaffi.

“Wannan sabon tsarin ya zama wanda zai haɗa ƙasa, ya kyautata shugabanci, ya kuma bunƙasa tattalin arziƙi. Duk wani gyara da za a yi ya zama wanda zai dace da burin jama’a da halin da ake ciki yanzu,” in ji shi.

Ya ambaci wani lauya a Amurka mai suna Cameron Smith, wanda ya jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana a cikin gwamnati.

“Dole ne mu kafa ƙa’idojin da za su bai wa kowa dama, rage rikice-rikice, da kuma samar da tsarin tarayya na gaskiya da adalci,” a cewarsa.

Ya kuma yaba da jagorancin Majalisar Tarayya da kwamitin sake gyaran kundin tsarin mulki saboda fara wannan muhimmin aiki, kuma ya bukaci a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.

“Ina roƙon kwamitin da ya tabbatar da cewa aikin yana tafiya cikin gaskiya tare da nufin karfafa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa,” in ji shi.

Ya kuma shawarci kwamitin da ya kasance bisa doron gaskiya da kishin ƙasa.

“Wannan lokaci ne na haɗin kai, ba na raba kawuna ba. Lokaci ne na kafa ginshiƙai domin gina Najeriya da kowa zai amfana da ita, ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko asali ba.

“Dole mu yi abin da zai haɗa kan al’umma, ya kawo adalci, da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa,” in ji shi.

Yayin da yake bayani kan rawar da Kano ke takawa a tsarin, gwamnan ya ce sun yi taruka da dama da al’umma, kuma za su miƙa cikakken rahoto nan ba da jimawa ba.

“Matsayin da Kano ke kai a wannan aiki ya samu ne daga haɗin gwiwa da jama’a, kuma muna shirin miƙa rahoton da ke ɗauke da ra’ayoyin al’ummar Jihar Kano,” in ji shi.