Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani dakin ajiye kayayyaki da aka makare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano.
Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a kofar rumbun da ke unguwar Kwakwaci a karamar hukumar Fagge da ke jihar.
Mojisola, wacce Daraktan Bincike da Tabbatar da Bin Doka na hukumar, Dokta Martins Iluyumade ya wakilta, ta ce dakin na dauke ne da lita 60,000 na sinadarin sulphuric acid, sai kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma wasu jarkoki 330 da aka riga aka rabar wa mutanen da ba a san ko su wane ne ba, sinadaran cikin su.
- NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum
- Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare
“Abin da muka gano yau a nan ya tayar mana da hankali matuka, ba na tunanin a rayuwata na taba ganin adadin irin wadannan sinadaran a waje daya,” in ji shugabar.
Ta ce jami’an hukumar ne tun da farko suka gano wajen, kuma ko da aka je, manajan da ke kula da wajen kawai aka tarar sai wani ma’aikacin wurin, inda aka kama su.
Ta kuma ce, “Ba mu da bayanan mamallakin wajen a matsayin dillalin wadannan sinadaran da gwamnati ta san da zamansa. Mukan ajiye bayanan dukkan masu wannan harkar domin mu rika sa ido a kan shige da fice da kuma amfani da wadannan sinadaran.
“Wadannan sinadaran suna da matukar hatsarin da bai kamata a ce kowa kawai na ta’ammali da su ba. A ka’ida dole sai mutum ya sami izini daga Ofishin mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkar Tsaro kafin ya fara shigo da su da kuma izinin mallakarsu, wanda babu daya daga cikin wadannan da mamallakin wurin yake da shi.
“Ana bukatar izinin ne saboda ana iya amfani da sinadaran wajen hada bama-bamai.
“Adadin sinadaran da muka gano a nan sun isa su tashi Kano gaba daya idan aka yi wasa da su,” in ji Mojisola.
Shugabar ta kuma ce yanzu haka suna ci gaba da titsiye mutanen da suka kama domin ganin an kama ainihin mamalakin wajen da ya riga ya cika wandonsa da iska don ya yi musu bayanin su wa yake sayar wa da sinadaran.
Sai dai ta ce za a bi hanyar da ta dace wajen lalata sinadaran bisa bin ka’idojin kiyaye lafiyar al’umma.