✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano

Wasu fusatattun matasa sun banka wa wani babur din Adaidaita Sahu da ake zargin na barayin waya ne wuta a unguwar Sharada da ke cikin…

Wasu fusatattun matasa sun banka wa wani babur din Adaidaita Sahu da ake zargin na barayin waya ne wuta a unguwar Sharada da ke cikin birnin Kano da safiyar Laraba.

Barayin da ake zargi dai sun shiga wata makaranta mai zaman kanta ne da ke Sharada mai suna Al-Abbas College, inda suka ce sun zo nema wasu yaransu gurbin karatu ne amma suka sace wayar shugaban makarantar.

Da yake zantawa da Aminiya, daya daga cikin malaman makarantar, Malam Sunusi Hamisu, da ya shaida yadda lamarin ya faru, ya ce, “Matasa ne guda biyu da suka ce sun zo neman gurbin karatu na yara guda biyu a aji biyu da aji uku na Firamare saboda sun ce sun canza gari ne sun dawo Kano daga Kaduna.

“To ni ne ma na raka su ofishin shugabar makaranta, sai ta ce a kai su ofishin mai makarantar, inda ya yi musu lissafin kudin rajista da na fom, sai suka ce ya dauko musu. To ya tashi zai dauko musu sai wayarsa ta fado, inda nan take suka dauke ta suka gudu.

“Fitarsu ke da wuya sai ya duba ya ga bai ga wayarsa ba, sai ya bi su da gudu ya karbi wayar, a lokacin har sun riga sun cire ta daga cikin gidanta sun cire layin sun kuma kashe ta.

“Da ya biyo su sai suka gudu suka shiga Adaidaita Sahun da suka zo da shi wanda ya tsaya a bakin titi yana jiran su. Nan take sai suka gudu a cikin babur din sai malamin ya fada wa mutane ga barayin waya, inda mutane suka yi kukan kura suka kama su.

“Da direban babur din ya ga an cim musu za a kama su, sai ya gudu ya bar babur din da barayin biyu a ciki, wadanda su kuma aka kama su,” in ji Malam Sunusi.

Ya ce bayan kama barayin ne aka mika wa ’yan sanda su, babur din kuma aka shigar da shi cikin makarantar.

To sai dai ya ce bayan an shigar da babur din ne sai matasan unguwa suka yi zuga suna barazanar balla kofar shiga makarantar idan ba a ba su babur sun kona ba, wanda ala tilas aka ba su suka fitar da shi suka banka masa wuta a bakin titi.

Shi ma wani mutum da abin ya faru a kan idanunsa mai suna Abdullahi Musa, ya ce an lakada wa barayin dukan tsiya kafin an damka su ga ’yan sanda sannan a kona babur din nasu.

“Mun riga mun yanke shawarar duk lokacin da muka kama babur din barayi sai mun kone shi, ta haka ne za su shiga taitayinsu,” in ji shi.