Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya koka kan yadda manyan motocin dakon kaya ke lalata babbar hanyar nan ta Maiduguri zuwa Ngamborun Ngala wacce ta hada Najeriya da kasashen Kamaru da Chadi.
A cewarsa, yawan daukan lodi fiye da kima da manyan motoci ke yi na kayayyakin masana’antu da kayayyakin masarufi a hanyar Maiduguri zuwa Gambouru, tamkar zagon kasa ne ga tattalin arziki.
- Dalilin da jihohi za su koma kayyade farashin kujerar Hajji — NAHCON
- Gwamnatin Tarayya za ta kafa kwamitin yaƙi da digirin bogi
Da yake nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda motocin ke lalata hanyoyin Gwamnatin Tarayya a garin Gambouru, ya bayyana cewa: “Yawan lodin manyan motoci dauke da kaya yana lalata hanyoyin wanda hakan zagon kasa ne ga tattalin arziki.
“Muddin ba mu ɗauki matakin da ya dace ba, to kuwa duk yadda za a gyara ko sake shimfida hanyar ba lallai ba ne ta yi karko ba wanda hakan zai sa mu koma gidan jiya.
“Hakika manyan motoci na kawo cikas ga kokarin Gwamnatin Tarayya na ingantawa da fadada ababen more rayuwa a jihar a bangaren sufuri da bunƙasar tattalin arzikin kasa.”
Dangane da yanayin tituna, ya ce: “Abin takaici ne a lura da abin da ke faruwa a kan manyan hanyoyin zuwa Kamaru, Chadi da Nijar.
“Kuna iya ganin tireloli cike da buhunan siminti ko sukari sama da 2,000. Wannan ya ƙunshi tan 100 na masana’antu da kayan gida na amfani yau da kullum wadda wannan yanayin Kai tsaye ya shafi hanyoyin na kan iyakokin da abin ya shafa zuwa kasashen makwabta.”
Ya koka da cewa an lalata hanyar Maiduguri/Gambouru/Ngala mai tsawon kilomita 135 saboda ɗaukar lodin manyan motoci fiye da ka’ida.
Gwamnan ya nanata illar hakan ga lafiyar jama’a da manyan motocin da suka yi makil a kan hanyoyin da abin ya shafa ke haifarwa.
“Akwai haɗari da ke tattare da direbobin manyan motocin da suke daukar lodin da ya wuce kima,” in ji shi, yana mai jaddada buƙatar aiwatar da tsauraran ka’idojin auna manyan motocin da ke bi ta gadoji.
Ya ce aikin auna nauyin motocin kafin su bi hanyoyin na iya kare manyan hanyoyin da kuma rayukan mutane daga shiga wani mummunan yanayi.
“A halin da ake ciki gadar nan da ta hade yankin iyakar Gamboru da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita na gab da rugujewa matukar ba a kiyaye ba,” in ji shi.
Ya ce gwamnatin jihar na shirin hada kai da hukumomin tarayya da abin ya shafa domin magance tabarbarewar hanyoyin kan iyaka.
“A yanzu haka an fitar da taswirar hanyoyi daban-daban, gami da aiwatar da tsarin auna nauyi, tare da aiwatar da hukunci kan masu karya doka,” in ji shi.
Zulum ya kara da cewa za a kafa tashoshi na musamman na motoci masu daukar kayan nauyin a wurare masu muhimmanci a kan manyan hanyoyin sufurin da ke jihar.
Ya kuma yi nuni da cewa, duk da kudurin gwamnati na habaka kasuwancin kan iyaka, za a aiwatar da matakan da suka dace don kula da hanyoyin sufurin.
A halin da ake ciki, gwamnan ya yaba da yadda Gwamnatin Tarayya ta yi na gyara hanyoyin da suka lalace a jihar wadda a cewarsa babban lamari ne na aiwatar abin da ya kamata.