✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum

Gwamnatin Borno ta ba da kimanin Naira biliyan 2 domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara ya bukaci Hukumar Raya Yankin Tafkin Chadi (CBDA) da ta sanya hannunjari sosai a fannin noman rani a kewayen yankin Tafkin Chadi, domin bunkasa wadatar abinci da kuma farfado da tattalin arziki a fadin jihar da kuma yankin Arewa maso Gabas.

Gwamna Zulum ya yi wannan kiran ne a lokacin da shugaban hukumar Farfesa Abdu Dauda Biu ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Da yake karin haske kan yadda ake noma a yankin, gwamnan ya bayyana cewa, gabar Tafkin Chadi, musamman yankunan da suka hada da Kirenowa da Marte da Gamborun Ngala da Baga suna da albarkatu masu yawa na ruwan karkashin kasa da kuma filayen noma da ya dace da noman rani.

“Ina so in ja hankalinku game da kasancewar ruwan kasa mai yawa a gabar Tafkin Chadi. Kada mu dogara ga ruwa sama kawai,” in ji Zulum.

Ya kara da cewa, “kwanan nan na aika da tawagar bincike don gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa.”

Gwamna Zulum ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta ba da kimanin Naira biliyan 2 domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga.

Sannan an ware ƙarin Naira biliyan 1.5 domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda dukkansu ke gab da kammaluwa.

“A kokarinmu na farfado da shirin noman rani na a Gabar Tafkin Chadi ta Kudu, a halin yanzu muna noman fili mai fadin hekta 1,000 a karkashin aikin noman rani na Baga a kan kudi kimanin Naira biliyan 2.

Bugu da kari, muna samar da hekta 200,000 a Gamboru da kuma wata hekta 200,000 na samar da wutar lantarki ta Lamboru ta hanyar amfani da tsarin ban-ruwa, don farfado da ayyukan noma a fadin yankin,” in ji zulum.

Farfesa Zulum ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa ta yi nasarar haka rijiyoyi kusan 3,000 a Damasak da ke Karamar Hukumar Mobbar, wanda hakan ya bai wa manoma damar yin noma a fili mai tsawon kilomita 16, matakin da ya bullo da hanyar noman ruwan karkashin kasa a yankin da a baya ba a saba da yin irin sa ba.

Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da hada kai da hukumar CBDA, domin fadada noman a Ngala da Damasak da New Marte da samar da ababen more rayuwa ga wadanda suka dawo da kuma tabbatar da dorewar samuwar abinci.

Ya kuma bayyana aniyar gwamnatin jihar na tallafawa wajen farfado da Tashar Famfunan Ruwa ta Chadi Basin Kirenowa, inda ya ce ana kokarin kafa bataliyar soji a yankin domin inganta tsaro.

“A matsayinmu na gwamnati, za mu so sanin inda za mu iya shiga saboda abubuwan da za a iya samu suna nan. Ina tuntubar Shugaban kasa da shugabannin sojoji kan yiwuwar kafa bataliyar soji a Kirenowa da nufin kare tashar famfon,” in ji Zulum.

A nasu jawabin shugaban hukumar Farfesa Abdu Dauda Biu da Manajin Darakta, Alhaji Tijjani Tumsa sun sanar da gwamnan cewa, an kafa sabuwar hukumar ce a ranar 13 ga watan Disamba 2024.

Sun bayyana cewa, sun ziyarci muhimman wurare da ke karkashin kulawarsu, ciki har da Madatsar Ruwa ta Alau, sun kuma yaba wa Gwamna Zulum kan yadda yake gudanar da ayyukanta.

Shugabancin Hukumar ta CBDA ya yi alkawarin hada kai da gwamnatin jiha don aiwatar da ayyukan da suka shafi noman rani da kiwon dabbobi da kamun kifi.

Sun kuma nemi goyon bayan gwamnan don ganin an kammala gyaran madatsar ruwa ta Alau a kan lokaci, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi a kwanakin baya.