✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Majalisar Dattijai ta yi ban kwana da Saraki

A ranar 11 ga watan Yuni mai zuwa ne ake sa ran za a kaddamar da sababbin ’yan majalisun dattawa da aka zaba da hakan zai…

A ranar 11 ga watan Yuni mai zuwa ne ake sa ran za a kaddamar da sababbin ’yan majalisun dattawa da aka zaba da hakan zai kawo karshen wa’adin ’yan majalisar dattijai da suka yi aiki a karkashin Sanata Bukola Saraki.

’Yan majalisar dattawa da suka yi aiki tare da Saraki ana musu lakabi ne da ’yan majalisa karo na 8 yayin da wadanda za su maye gurbinsu kwanan nan za su kasance ’yan majalisa karo na 9.

Sai dai abin da ya fi daukar hankali da kuma ban sha’awa shi ne yadda majalisa karo ta 8 ta gudanar da aikinta cikin kwarewa da basira da kuma hangen nesa a karkashin shugabancin Sanata Bukola Saraki.

A lokacin shugabancin Bukola Saraki, majalisar ba za ta taba manta irin namijin kokarin da ya yi wajen samar da dokokin da suka taimaka wajen habaka tattalin arzikin Najeriya ba.  Bisa hangen nesansa da kuma iya shugabanci Bukola Saraki ya samar da dokokin da suka taimaki kasar nan wajen habaka tattalin arziki a bangarori da dama da suka hada da na samar da ayyukan yi da bunkasa ilimi da inganta tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas da kuma a bangaren kula da kiwon lafiya.

Duk da majalisar Saraki ta samu nakasu a yayin gudanar da aiki a wasu lokuta amma ganin yadda kwararren shugaban ya yi amfani da juriya da hangen nesa ta sa ya dora majalisar a ingantacciyar turba da ake ganin majalisa mai zuwa ta amfana.

Sai dai tarihi ba zai taba manta yadda Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar ba, duk da irin adawar da ya fuskanta daga wajen Jam’iyyarsa ta APC (kafin ya koma PDP).

Wannan ya sa jam’iyyarsa ta APC ta rika yi masa bi-ta-da-kulli da suka hada da kai shi kara gaban kotun da’ar ma’aikata (CCT) a zargin da ake masa na kin bayyana kadadorin da ya mallaka kafin ya zama shugaba da sauransu.

Ko shakka babu, Bukola ya zama zakaran gwajin dafi a siyasar kasar nan, wanda za a dade ba a manta da shi ba musamman yadda ya kawo ci gaba a fannin farfado da tattalin arzikin kasar nan da kuma a bangaren samar da tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas.