✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mai shekara 40 ta haifi ’ya’ya 44

A yanzu haka ita ke kula da ’ya’ya 38 gaba daya, kasancewar shida daga cikin 44 sun mutu.

Wata mata mai suna Ify Mado a kasar Uganda, ta haifi ’ya’ya 44, a yayin da take da shekara 40 a duniya.

A yanzu haka ita ke kula da ’ya’ya 38 gaba daya, kasancewar shida daga cikin 44 sun mutu.

Wani Balarabe mai kirki ne ya samar da gadajen da ’ya’yanta ke kwana kuma wata da ake kira Mama Uganda ta samu damar taimakon sanya ’ya’yan duka a makaranta.

A rayuwarta, sau daya ta haifi yaro daya, duk sauran sun kasance tagwaye da ’yan uku da ’yan hudu.

Ta haifi maza 22 da mata 16 wadanda har yanzu suna raye.

Jimillar haihuwarta 44 ta kasance ta haifi tagwaye sau 4 sai ’yan uku sau 5, sai ’yan hudu sau 5 idan an hada da da guda da ta haifa a baya.

Wani mai bincike mai suna Hattab da ya ziyarci gidan matar kuma ya wallafa bidiyon a kafofin watsa labarai sun yi ta martani game da rayuwar Ify da iyalanta, inda suka ce, “gaskiya matar jaruma ce.

“Ya kamata ta shiga cikin littafin kundin tarihin duniya (Guinness Book of Records). Bayan haka ya kamata Shugaban Kasar Uganda ya dauki nauyin jin dadin iyalin gaba daya.

“Dole ne ta shiga cikin tarihin duniya, domin Allah ne kadai zai iya daukar nauyin rayuwar iyalan.

“Akalla idan ana magana kan tarihin Uganda tabbas za a ambaci matar. Wannan ba kasafai ake samun sa a duniya ba. Ina taya ku murna. Allah Ya ci gaba da azurta iyalanki.”

Natasha Ibrahim ta rubuta cewa: “Allah Ya azurta ta da ’ya’yanta. Ba zan iya rayar da abin da na haifa ba, ni da nake da juna biyu dauke da da guda.

“Dadin haihuwa a kodayaushe ta koma gida akwai masu jiran ta. Irin wannan haihuwar baiwa ce.”

Martanin Mary-Anne Delaney kuwa shi ne: “Mahaifiyar ’ya’yan tana da kyau sosai. ’Ya’yanta suna cikin murna. Duk da haka, suna bukatar samun tallafin kudi.

“Akwai bukatar a canja dokokin kasar game da yin auren wuri. Allah Ya albarkaci iyalansu.”