✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mai shayi ya zama dan Majalisa a Kano

Hon. Mudassir Ibrahim Zawachiki shine mamba mai wakiltar Kumbotso a Majalisar Kano, ya yi sana’ar sayar da shayi har ya zama dan majalisa.

Hon. Mudassir Ibrahim Zawachiki shi ne mamba mai wakiltar Mazabar Kumbotso a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Acikin wannan tattaunawar da Aminiya, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya yi gwagwarmaya daga sana’ar sayar da shayi har zuwa lokacin da ya zama dan majalisa.

Ku biyo mu:

Ko za ka iya gabatar mana da kanka?

To ni dai suna na Hon. Mudassir Ibrahim Zawachiki, ni ne Mamba Mai Wakilar Mazabar Kumbotso a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Na yi karatu a Kwalejin Rumfa da ke Kano daga bisani kuma na wuce zuwa Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano inda na karanci Aikin Jarida.

An zabe ni a matsayin Kansila mai wakiltar Mazabar Panshekara kuma Shugaban Kansiloli a wannan Karamar Hukumar ta Kumbotso.

Daga bisani kuma an zabe ni a matsayin Dan Majalisa mai Wakilar Kumbotso karkashin Jam’iyyar PDP a shekarar 2019.

Kafin ka shiga siyasa, ko akwai wata gwagwarmayar sana’a da ka yi?

Alhamdulillah, tun ina dan karami, mahaifina wanda dan kasuwa ne a kasuwar Singa da ke Kano kuma yana sana’ar sayar da hatsi da sauran kayan abinci. To na kan bi shi kuma in koyi sana’a.

Daga baya kuma sha’anin rayuwa abubuwa suka canza sai na yanke shawarar neman mafita saboda ba zai yiwu mutum ya zauna haka kawai ba.

Daga nan ne na tsunduma sana’ar sayar da shayi, duk da haka kuma ina ci gaba da bin mahaifin nawa wurin sayo hatsin.

A zahirin gaskiya ma kusan har da na zama dan majalisar na kan bi shi zuwa wasu jihohi kamar Taraba, Adamawa da Gombe domin sayo hatsi kamar masara, shinkafa da gyada.

Mutane da dama za su yi mamakin ka taba sayar da shayi la’akari da matsayin da kake kai yanzu. Wane darasi ka koya har ka yanke shawarar shiga sana’ar?

To Alhamdulillah, shi Allah a kullum Yakan duba zuciyar mutum in niyyarsa mai kyau ce.

Ni gaskiya tun kuruciyata ba abin da nake so kamar sana’a —A kullum tunanina bai wuce yadda zan juya kwandala ta koma Naira 10 ba.

Mahaifina yakan kai ni shago tun ina yaro, tun ban ma iya kirga kudi ba, mukan sayi hatsin da ya kai kusan buhu 200 (a wancan lokacin), amma duk da haka yakan ajiye ni a sahgon har sai da ta kai lokacin da sai dai kawai a turo min da kaya na tura masa kudi in suka kare.

A rayuwa, duk a inda ka tsinci kanka kawai ka gode wa Allah.

Lokacin da abubuwa suka canza a harkokin sana’ar mahaifina sai na yanke rungumar sana’ar shayi, tun a lokacin ma ina matakin karatun sakandare.

Na kan hada sana’ar da zuwa makaranta a lokacin.

Amma babban ginshikin dai shi ne kada mutum ya raina kowacce irin sana’a.

Ni abind na yi amanna da shi shi ne ba na raina kowace irin sana’a komai kankantarta.

Ko a lokacin da na shiga siyasa, wasu kawai sai su kalle ni su ce, “Sai Mai Shayi” ni kuma sai in yi dariya in amsa musu, saboda sana’ata ce kuma ina alfahari da ita.

A duk cikin sa’o’i na mutum shida, wasu ma’aikatan gwamnati ne, wasu malaman makaranta, amma abin mamaki babu wanda ba ya zuwa wurina aron kudi, duk albarkacin wannan sana’ar ta shayi.

Hatta gidan da nake ciki a yanzu haka da sana’ar na gina shi.

A wancan lokacin, don kana ma’aikaci mai daukar N150,000 a wata zan iya ja da kai.

Nakan iya yin cinikin N70,000 zuwa N100,000 a kullum.

Ba na shayin yin kowace irin hidima daga N1,000 har zuwa N100,000 a lokacin.

Na yi sa’a na samu wuri a fuskar jama’a kuma mutane na zuwa wurina sosai, ana ciniki.

Alhamdulillah, Allah Ya albarkaci kasuwancin nawa sosai, akwaiyara da yawa a karkashina.

Ta kai lokacin da ko ban je rumfar ba yarana za su kula da komai saboda yaran nawa za su kula da duk abin da ya kamata.

Mutum nawa ne suke aiki karkashinka a lokacin?

Akwai yara shida a karkashina a lokacin.

Shin har yanzu wurin yana nan kuwa la’akari da matsayinka na yanzu?

Kwarai kuwa, har yanzu yana aiki.

Ko ma kafin na bar wurin, uku daga cikin yaran da ke aiki a karkashina sun bude wurarensu, amma har yanzu babbar rumfar tana nan tana aiki.

Akwai kanina da yanzu haka yake kula da wajen Kuma Alhamdulilah yana ci gaba da kula da shi har ma ya kammala karatun NCE duk da wurin.

Ganin yadda yanzu Allah Ya albarkaci sana’arka har ka kawo matsayin da kake kai yanzu, wane sako kake da shi ga matasa?

Ina kira gare su da kada su sake su raina kowace irin sana’a.

Yawancinsu suna da tunanin yin kudi a dare daya ba tare da yin sana’a ba.

Ita sana’a kuma tana bukatar hakuri da juriya ta yadda za ka ci gaba da kula da kwastomomi da ma shi kansa kasuwancin naka.

Matasa su daina kallon masu kudi kawai suna son zama kamarsu ba tare da duba gwagwarmayar suka sha ba.

Ba ka san wahalar da mai kudi ya sha ba kafin ya tara su ba, saboda haka dole sai mutum ya yi hakuri.

Akwai abubuwa biyu da na yi la’akari da su da ke zama kalubale ga matasanmu a yau: na farko idan suka fara sana’a yau, so suke gobe su yi kudi; na biyu kuma akwai masu kudi da yawa da ke son fara sana’a amma suna fargabar wanda za su dauka ya rike musu amana.

Yawancin matasanmu a yau sun gwammace su rika sayen manyan wayoyi da suturu masu tsada, shi kuwa kasuwanci bai gaji wannan ba.

Dole ka ware uwa ka ware riba kafin ka san nawa za ka kashe.

Duk wanda yake kashe sama da abin da yake samu to tabbas kasuwancinsa babu inda zai je.

Amma idan mutum ya yi hakuri, da sannu sai ya kai ga inda yake burin kaiwa.

Ya kamata matasanmu su yi koyi da irin su A.A. Rano.

Na taba ji ana hira da shi ya ce har tallan manja ya taba yi da sauran sana’o’i; Yanzu dubi inda Allah Ya kai shi.

Mutum ba zai iya kauce wa abin da Allah Ya tsara masa ba.

Ina kira ga matasa musamman na Kano su yi amfani da damar kasuwancin da ke a garin kasancewarsa cibiyar kasuwanci ba a iya Najeriya kadai ba. Kusan ko ina a Kano yanzu kasuwa ne.

Mutum zai iya farawa da wata ‘yar karamar sana’a a cikin unguwarsu, in ta bunkasa daga nan sai ya canza ya koma wacce yake hari, wata rana sai ka ga Allah Ya sa albarka a ciki ta bunkasa.

A kullum Allah Yakan duba kyawun niyyar mutum.

A matsayinka na ganau ba jiyau ba, ko akwai wani yunkuri da kake yi na tallafa wa matsa su ma su bi sahunka?

Kusan kullum mu dama akidar siyasarmu kenan ta tallafa wa mutane.

A kullum kuma muna tallafa musu su tsaya da kafafunsu.

Burina shi ne har kullum in ga mutane na ci gaba, ina so in ga wani a inda na bari.

Amma babban jigon dai shi ne dole mutum ya bi hanyar da ta kamata ya kuma hada da hakuri.

Yau ga ni a nan, gobe kuma wani ne a wurin.

Ina fatan ganin duk wanda ya taka wata rawa wurin cigabanmu shi ma an tallafa masa.