✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Mahauci Ya Kashe Matarsa Saboda Wayar Hannu A Adamawa

Ya bayyana nadamarsa dangane da kashe matarsa da ta haifa musu yaro ɗaya.

Ana zargin wani mahauci Ibrahim Abubakar mai shekaru 33 da kashe matarsa Hajara Sa’adu ‘yar shekara 25, ta hanyar caccaka mata wuka ta ƙeyarta.

Tuni dai ’yan sanda sun kama wanda ake zargi da aikata wannan ɗanyen aiki a Sabon Gari Duti da ke Karamar Hukumar Girei a Jihar Adamawa.

Wani mazaunin yankin da abin ya faru mai suna Abubakar, ya ce wanda ake zargin ya cakawa matarsa wuka mai kaifi a baya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar ranar Litinin, 8 ga Afrilu, 2024.

Bayanai sun ce Abubakar ya zargi matarsa da ɗauke masa wayarsa, daga bisani suka samu rashin jituwa, wanda daga nan ya hasala ya ɗauko wuka ya burma mata a wuya ta baya.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar ’yan sandan Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar ya ce; “Abubakar ya yi wa matarsa kisan wulakanci, kuma ya barta cikin jini.”

SP Nguroje ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan mahaifin matar da aka kashe ya miƙa korafi.

“A lokacin da ake gudanar da bincike, an gano wukar da Abubakar ya yi amfani da ita a wurin da ya aikata laifin.”

Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya bayyana nadamarsa dangane da kashe matarsa da ta haifa musu yaro ɗaya.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris ya bayyana rashin jin daɗinsa kan faruwar lamarin

Ya kuma ba tabbacin cewa rundunar za ta tabbatar da gurfanar da mai laifin a gaban kotu domin a yi masa hukuncin da ya yi daidai da laifinsa.

Ya kara da cewa, “A namu bangaren, muna iya ƙoƙarinmu wurin dakile miyagun laifuka a jihar.”

SP Nguroje ya buƙaci jama’a da su kai rahoton mutanen da ke nuna munanan dabi’u a unguwanni ga ‘yan sanda.