✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumar Kannywood Daso ta rasu

Mutuwar fuju’a ce ta riski Daso daga kwanciya barci bayan ta yi sahur.

Allah Ya yi wa jarumar Kannywood, Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito ’yan uwan Daso na cewa mutuwar fuju’a ta riske ta daga kwanciya barci bayan ta yi sahur.

Daso wadda ta rasu tana da shekara 56 an haife ta ne a ranar 17 ga watan Janairun 1968 a birnin Dabo.

Jarumar ta shahara wajen fitowa fina-finai na barkwanci da nuna kisisina irin ta ’ya’ya mata.

Fim na farko da Daso ta fito shi ne Linzami da Wuta wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya a shekarar 2000.

Sauran fina-finan da suka ƙara haska tauraruwar Daso sun haɗa da Nagari, Gidauniya, Mashi da kuma Sansani.

Aminiya ta samu rahoton cewa za a yi jana’izarta nan gaba kaɗan da misalin ƙarfe 4:00 na Yamma a Kano.