✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ma’aikatan lafiya ke kamuwa da COVID-19 a Najeriya

Ma’aikatan lafiya 47 ne gwamnatin Kano ta tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a jihar. Jagoran kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar COVID-19…

Ma’aikatan lafiya 47 ne gwamnatin Kano ta tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a jihar.

Jagoran kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar COVID-19 Dokta Tijjani Hussain ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Lahadi.

Sai dai ya ce ma’aikatan lafiyar sun kamu ne a makwannin baya, domin a ’yan kwanakin nan ba a samu wanda cutar ta kama ba.

Ya kara da cewa a yunkurinta na shawo kan annobar, gwamnatin jihar na bayar da horo ga ma’aikatan lafiya na sahun farko su fiye da 1,000.

Gudun majinyata

Yadda ma’aikatan jinya ke kamuwa da cutar ne dai ya sa daruruwan jami’an kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a fadin Najeriya ke guje wa marasa lafiya, kamar yadda wani binciken jaridar Aminiya ya nuna, saboda ba su da kayan kariya daga kamuwa da cutar.

Kayan kariyar dai sun hada da takunkumin rufe fuska da safar hannu da rigunan kariya da tabarau da bututun shakar iska da kuma takalmi maciji sari banza.

Wasu likitoci da ma’aikatan jinya da masu aiki a dakunan gwaje-gwaje sun tsinci kansu a wuraren killace wadanda suka kamu da COVID-19 bayan gwajin da aka yi masu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar, yayin da wasun su da dama kuma suka killace kawunansu a gidajensu a daidai lokacin da suke jiran sakamako gwajinsu.

Cutar ccoronavirus ta shammaci kasashen duniya ciki har da Najeriya inda asibitoci ba su da kayan aiki ba kuma tanadin ko ta kwana.

Duk da dai an samu ci gaba ta fuskar inganta wuraren killace jama’a don yaki da cutar COVID-19 ta hanyar kwamiti na musamman da gwamnatin tarayya ta kafa da kuma tallafin da wasu ‘yan kasa da kuma wasu daga kasashen waje suka bayar, Aminiya ta gano cewa har yanzu babu isassun kayan kariyar, lamarin da ya sanya ma’aikatan lafiya da dama suka kamu da cutar yayin da majinyata da dama ke mutuwa saboda rashin samun kula daga likitoci.

Rashin kayan kariya

Akwai asibitocin gwamnatin tarayya 22 a fadin Najeriya, kuma galibin su suna ikirarin samar wa da likitoci da ma’aikatan jinya isassun kayan aiki na kariya.

Masu magana da yawun asibitocin da ke Ebonyi da Bayelsa da Legas sun shaida mana cewa suna da kayan aiki na kariya isassu da suka sama wa duk ma’aikatansu.

Sai dai wannan batu nasu ya yi hannun riga da bayanan da su kuma ma’aikatan lafiyar wadannan jihohin suka fada.

Daya daga cikin ma’aikatan lafiyar a jihar Legas da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an ba su sabon takunkumi na N95 ne a ’yan kwanakin nan, domin haka wasunsu sukan sanya takumkumi daya suna aiki da shi har tsawon makonni.

“Ka kuwa san komai kyawunsa dole zai iya daukar kwayoyin cuta.

“Amma su mahukuntanmu suna fada mana cewa wai babu wani abu da zai faru don an yi amfani da takumkumin sau da yawa”, inji shi.

Asibitoci ba sa karbar marasa lafiya

Haka kuma bincike ya nuna cewa ba kowane asibiti ba ne yanzu suke karbar marasa lafiyar da aka kawo ranga-ranga.

Sannan su ma asibitoci masu zaman kansu a wasu jihohin sun daina karbar kowanne irin marar lafiya, domin suna ganin wannan wani mataki ne da zai kare ma’aikatansu daga kamuwa da cutar coronavirus.

Dokta Ali, wani likita da ke duba marasa lafiya a asibitin gwamnati da kuma asibitoci masu zaman kansu   Abuja da wasu jihohi, ya ce wannan shi ne mawuyacin hali mafi muni da suka taba samun kansu a ciki.

“Muna son marasa lafiya, kuma a shirye muke ko da yaushe mu taimake su, amma saboda matakan kare kanmu da iyalanmu dole muke takatsantsan”, inji shi.

‘Za mu iya aiki ne idan da kariya’

Ya ci gaba da cewa, “Za mu iya aiki ne idan har muna da kariya, amma a gaskiya yanzu muna cikin fargaba.

“Mun yanke shawarar rage yawan marasa lafiyar da za mu dinga dubawa, a yayin da a wasu lokutan ma ba za mu duba su ba gaba daya saboda ba mu da kayan sawa na kariya daga kamuwa da wannan cuta wadanda a ka’ida sau daya ake so a sanya su sai a cire a yar, amma ka ga yanzu muna aiki da su fiye da hakan.

“Wasu lokutan ma’aikatan lafiya kadan ne kawai ke ma samun kayan kariyar. In kuma ka yi la’akari da yadda cutar take yawan yaduwa cikin jama’a, za mu iya cewa kowanne marar lafiya zai iya zuwa da cutar, don haka kasada ce ka duba shi ba tare da ka sanya kayan kariyar ba.

“Gwamnatin tarayya ka kawo kayan kariyar, amma fa ba su isa ba. Kowanne asibiti ya kamata a ce yana da su isassu ko da kuwa ba ya cikin wuraren duba masu fama da cutar ta COVID-19.

“Na yarda cewa wasu abokan aikinmu suna dar-dar da majinyata, ba na son in ce suna kaurace wa majinyata, amma wannan mataki ne da ya zama tilas har sai mun samu kayan sawa na kariya”, inji Dokta Ali.

‘Tsoron daidai ne’

“Tsoron da muke nunawa a nan daidai ne”, inji wani likita da baya son a ambaci sunansa.

Ya kuma tabbatar wa Aminiya cewa akwai abokan aikinsa da dama da suka daina zuwa aiki saboda babu kayan kariya.

Ya kuma ce akwai da dama daga cikin abokan aikinsa da aka gwada su aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 din, yayin da wasunsu kuma suke zaman jiran jin nasu sakamako.

“Mafi munin abin shi ne, wata abokiyar aikinmu da ta kamu da cutar kuma ta watsa wa mahaifiyarta.

“Mun yanke shawarar mu kaurace wa wuraren aikinmu saboda mun kai koke wa shugabannin asibitin na karancin kayan kariyar amma babu abin da suka yi a kai.

“Rayuwarmu da ta iyalanmu tana cikin garari haka kuma ta marasa lafiyar. Mun gode Allah shugabannin asibitin sun fara daukar mataki.

“Amma duk da haka ba za mu dawo ba sai an fitar da sakamakon gwajin abokan aikinmu, don mu san su wa da wa ya kamata su koma bakin aiki kuma su wa za a killace.

“Ya kamata shugabannin asibitin su samar da otal din da likitoci za su zauna na tsawon mako biyu ga wadanda suka gama aikinsu na mako biyu a baya, ta yadda ba za su koma cikin iyalansu ba har sai sun san sakamakonsu.

“Haka ake yi a Abuja kuma tsarin yana aiki daidai,” inji shi.

‘Muna cikin hadari’

Wani likitan kuma cewa ya yi ba sa karbar marasa lafiya a yanzu saboda abokan aikinsu da dama sun kamu da cutar.

“Haka abin yake ma a nan asibitin Dala. A cikin likitoci 25 da aka yi wa gwajin, 15 sun kamu da cutar; wallahi muna cikin hadari”, inji shi.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) reshen Jihar Kano ya bayyana cewa da yawan wadanda cuyar korona ta Kama a likitoci ne da suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Daraktar yada labarai ta Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, Hajiya Hauwa Muhammaed Abdullahi, da take tsokaci a kan lamarin ta ce hukumar asibitin ta yi bakin kokarinta wajen ba da kariya ba ga likitoci kawai ba har ma da sauran ma’aikata.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Kasa, Dokta Francis A. Faduyile, cewa ya yi kungiyarsu ta yi ta nanatawa cewa babu isassun kayan kariya a asibitocin da ke fadin kasa.

Ya ci gaba da cewa ko da ma su kansu cibiyoyin killace masu cutar COVID-19 din suna fama da karancin kayan sawa na kariyar.

Yawan ma’aikatan da suka kamu

Da aka tambaye shi ko yana sane da cewa likitoci suna kaurace wa wuraren aikinsu saboda karancin kayan na kariya, sai ya ce ba shi da masaniyar hakan.

Ya ci gaba da cewa ma’aikatan lafiya 113 da Ministan Lafiya ya ce sun kamu da cutar ba su hada da likitoci shida da sakamakon gwajinsu ya nuna suna dauke da cutar ba a Legas da kuma wasu 30 da suka kamu da ita a Kano ’yan kwanaki bayan ministan ya yi jawabi ba.

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Kasa (MHWUN) ta fitar da sanarwar cewa kimanin mambobinta 100 ne suka kamu da cutar COVID-19.

Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su samar da isassun kayan sawa na kariya ga ma’aikatan lafiya a fadin kasar nan.

Sanarwar ta ce “Yin wannan yana da matukar muhimmanci saboda ma’aikacin lafiya ba dan kunar bakin wake ba ne, sai ya kasance yana da rai da lafiya ne zai iya duba marasa lafiya.”