Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar.
Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
- Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno
- An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara
Kamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara.
“Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta.
Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 255 tare da samar da kayan aiki na zamani da magunguna.
Wannan zai bayar da damar kula da cututtuka kamar su ciwon suga, hawan jini, da kuma bayar da agajin gaggawa ga mata masu naƙuda.
“Ingantaccen kiwon lafiya ba gata ba ne, haƙƙi ne,” in ji Hajiya Umma, yayin da ta ke jadadda ƙudirin gwamnatin jihar kan kiwon lafiya.