✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda uba da ɗansa da wani ango suka rasu a bakin aiki a Bauchi

Wasu jami’ai da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Gubi, sun bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani uba da dansa da kuma wani…

Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi guda huɗu sun rasu a yayin da suke aikin tsabtace madatsar ruwa ta Gubi.

Wasu jami’ai da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Gubi, sun bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani uba da dansa da kuma wani wanda ke shirye-shiryen ɗaurin aurensa.

“Abin ya faru ne a lokacin da suke aikin tsaftace ruwan da ake kula da ruwan da ake yi wa babban birnin Bauchi. Na samu labarin suna cikin tafki, sai suka ga wasu kifaye a cikin ruwan datti, ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin kama kifi, kifin ya yi zurfi, sai ya bi shi ya mutu.

“Ana cikin haka, wani abokin aikinsa da ya ga abin da ya faru ya yi ƙoƙarin ceto shi, shi ma ya mutu, kuma anyi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ta tanada,” kamar yadda wani abokin aikinsu ya bayyana.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce ma’aikatam da suka rasu sun hada Shayibu Hamza mai shekaru 48 da Abdulmalik Yahya mai shekaru 29 da Jamilu Inusa mai shekaru 29 da kuma Ibrahim Musa mai shekaru 42.

Ya ci gaba da cewa lamari mai ban tausayi ya auku a madatsar ruwa ta Gubi, wanda ya yi sanadin asarar ma’aikatan da suka sadaukar da kansu a yayin wani aikin yashe shara da ke cikin ramuka a madatsar ruwan ta Gubi.

Ya ce A lokacin da waƙi’ar ta auku, an yi ƙoƙarin ceto su, aka fito da su a sume daga cikin ramin tara ruwan da suke aikin, daga nan aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi, amma duk da kulawar gaggawa da aka ba su, sai Allah Ya karɓe su, likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Wakil ya ce, a lokacin da ’yan sanda suka samu labarin faruwar lamarin, sun tura jami’ai zuwa wurin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru.

Ya ce akwai buqatar qara daukan matakai a vangaren kula da ruwa, yana mai jaddada muhimmancin dukkan ma’aikatan su kula da bin ƙa’idojin aminci da aka kafa don rage haɗari nan gaba.

Duk ƙoƙarin da muka yi na jin ta bakin Kwamishinan Albarkatun Ruwa ma Jihar Bauchi, Abdulrazaq Nuhu Zaki, da Babban Manajan Kamfanin Samar da Ruwan Sha na Jihar Bauchi, Injiniya Aminu Aliyu Gital, a game da lamarin ya ci tura.