An tabbatar da rasuwar mutum uku tare da asarar gonakin shinkafa da faɗinsu ya kai hekta dubu 10 a Jihar Neja a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.
Wannan ibtila’i ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mokwa, sakamakon sakin ruwa da hukumomi suka yi daga Madatsar Ruwa ta Jebba da ke jihar.
Shaidu sun bayyana cewa ambaliyar ta yi ɓarna sosai a gonakin yankin.
Shugaban Ƙungiyar Raya Yankin Kede, Abdulraham Abdulƙadir Kede-Wuya, ya ce gonar shinkafarsa mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda suka salwanta a ambaliyar.
- Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno
- An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi
Ya ce, “gonata mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda ruwan ambaliyar ya shanye, Sannan akwai sauran masu gonaki. Duk gonakin da bain ya shafa sun kai lokacin girbi. Ba mu san abin da ya da suka saki ruwan a irin wannan lokaci ba tare da sanar da al’umma ba.”
Wani manomi a yankin, Ibrahim Ndako, ya bayyana ambaliyar a matsayin bala’i, yana mai kira ga hukumomi su kawo musu ɗauki.
Ibrahim ya bayyana cewa, “Irin asarar asarar rayuka da maƙudan kuɗaɗe da wahalhalun da manoman rani suka tafka a sakamakon wannan abu, da wuya a iya mayar da shi.”
Ya ce yawancin manoma sun zo yankin ne daga jihohi Kebbi, Sakkwato, Zamfara Kano da Borno, domin yin noman rani a yankin, amma yanzu an jawo musu asarar.
Aminiya ta samu labarin cewa wasu daga cikin manoman sun fara girbi a lokacin da ambaliyar ta auku.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Aufu Hussaini ya ce an samu asarar rayukan ne a lokacin da wani kwalekwale ɗauke da su yake ƙoƙarin tsallake kogi da su bayan ambaliyar.
Ya bayyana cewa hukumar tana ci gaba da bincike domin tantance girman asarar da aka yi a sakamakon ambaliyar.