Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi wa Manchester United wankin babban bargo da ci biyar da nema har gida.
Kungiyoyin sun barje gumi ne a gasar Firimiyar Ingila a ranar Lahadi.
- Jami’o’in Arewa 3 za su ci gajiyar shirin Bankin Duniya
- “Juyin mulki”: An tsare shugabannin farar hula na gwamnatin Sudan
Manchester United na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga magoya baya, inda ake sukar mai horar da kungiyar bayan rashin nasara da ta yi a hannun Leceister City a makon da ya gabata.
Liverpool ta yi bajinta, inda dan wasan gabanta Mohamed Salah ya zura kwallaye uku rigis a wasan.
Dan wasan tsakiyar Manchester United, Paul Pogba ya samu jan kati a minti na 59, bayan mummunan taku da ya yi wa dan wasan Liverpool, Naby Keita.
Yanzu haka dai, kungiyar ta Manchester United, na matsayi na bakwai a teburin gasar Firimiya, inda take da maki 14 daga wasanni tara da ta buga.
Yayin da ita kuma Liverpool ke matsayi ma biyu, da maki 21 daga wasanni tara da ta buga.