Yakin Boko Haram a Arewa maso Gabas da ayyukan ta’addanci na ’yan bindiga, sun sa mutane da dama sun zama ’yan gudun hijira, inda suke zaune a sansanonin gudun hijira a cikin wasu alkaryu da birane bayan sun gudo daga kauyukansu.
Kasancewar yawancin mutanen sun baro kauyukansu da garuruwansu ga kuma karancin samun tallafi daga gwamnati, sai abinci ya zamo wa wadansu da dama babbar wahala, inda wadansu mazan suke yi ayyukan karfi don samun abinci.
- Muhimman abubuwa 12 daga jawabin Buhari kan zanga-zangar #EndSARS
- Sultan ya roki limaman Juma’a su yi hudubar zaman lafiya
Binciken Aminiya ya gano cewa a wasu sansanonin gudun hijira, akan tilasta wa mata shiga ‘karuwanci,’ ta hanyar ba da kansu, domin su samu kudin abinci.
Jihar Borno
Aminiya ta ziyarci wani sansanin gudun hijira a garin Bama da ke Jihar Borno, inda a zantawar da ta yi da wata budurwa da abin ya shafa ta bayyana mata cewa dole ne ta sa suke bayar da kansu ga maza, idan ba haka ba sai mutum ya mutu da yunwa.
Ta kara da cewa ba sa samun tallafin da ya kamata, sannan akan dauki lokaci mai tsawo kafin su sake samun abinci, wanda hakan ya sa wadansu a dole sai sun ba da kansu don samun abin sakawa a baki.
Budurwar wadda aka sakaye sunanta ta kara da cewa idan sun fita akwai samari da a kullum suke bukatarsu, kuma ba wani kudin kirki suke ba su ba.
Sannan ta ce a cikin jami’an tsaro akwai masu hulda da su kuma a sansanin akwai ire-irenta da dama.
Sai ta yi kira ga hukumomi su rika ba su tallafi a kan lokaci domin idan ba a dauki mataki ba, za a samu yawaitar ’ya’ya ba ta hanyar aure ba, wanda zai iya zama barazana ga zaman lafiyar da ake kokarin samarwa.
Wata da Aminiya ta yi kicibis da ita, a daidai Sakatariyar Karamar Hukumar Bama, ta ce wannan abu na lalata da mata ’yan gudun hijira a sansanonin ba wani sabon abu ba ne.
Domin a cewarta, tun bude sansanin gudun hijirar ake samun wannan matsalar, “An raba mu da garuruwanmu ba mu da kowa.
“Sai da na shafe kusan wata takwas a hannun Boko Haram kafin Allah Ya kubutar da ni.
“Kusan shekara shida ke nan ba mu da labarin iyayenmu, ko suna raye ko sun mutu sai Allah.
“A gaskiya ba na yin lalata don neman abinci, sai dai ina bara; Amma akwai ’yan mata da manyan mata da ba a bar su ba a wannan harka, don akwai wadanda na sani.
“Ya kamata a samu wata hanya ta kara ba da tallafin don ceto mutuncinsu,” inji ta.
‘Mata biyu suka haihu a makon shekaranjiya’
Wani dattijo Malam Goni Bama Dina da Aminiya ta zanta da shi ya ce matsalar babba ce, don a kullum ana samun yara mata da suke haihuwa a sansanin, inda ya ce bai yarda talauci ko rashin abinci ne dalilin da zai sa mace ta mayar da kanta tamkar akuya don ta samu abinci ba.
“Ko a makon nan (makon shekaranjiya) mata biyu suka haihu kuma aka daura musu aure da wanda suka yi musu cikin daga baya.
“Har ta kai wani lokaci mu manyan mukan sa a rika zagawa don hana wannan lalata, wanda kusan kowane dare ake yin ta, baya ga masu fita waje, su aikata lalata su dawo.
“Lamarin dai ya kasance abin damuwa”, inji shi.
Aminiya ta hadu da wata mata a kusa da sansanin gudun hijira na hanyar Gwoza.
Ta ce akwai ’yarta da wani saurayi ya yaudare ta ya yi mata ciki, abin da ta haifa ya koma, sannan ta ce a kullum kara kazanta abin yake yi.
Wani sansani mai zaman kansa da Aminiya ta leka ta gano cewa akwai wadansu ’yan mata da suke dauke da ciki babu aure.
Wani matashi da Aminiya ta zanta da shi ya ce matsalar ta zama ruwan dare a sansanin.
‘Ana yaudarar ’yan matan ne da batun aure’
Matashin ya ce akan yaudari ’yan matan ne da zancan aure, amma a karshe da matashi ya samu biyan bukatarsa shi ke nan sai ya yi watsi da ita, ko ya bar sansanin ya sauya sheka.
Wani matashi mai suna Zanna Kachalla cewa ya yi akasarin lokaci ’yan matan ne suke jefa kansu a cikin wannan matsala, domin da zarar namiji ya nuna yana son mace, nan take babu wani bincike sai ta mika masa wuya.
Lamarin akwai ban takaici —Masani
Wani masanin zamantakewa Malam Muhammad Sani ya ce yanayin da ake ciki a wasu sansanonin gudun hijira na Jihar Borno abin takaici ne, inda ya ce a lokacin da suka gudanar da wani aiki a daya daga cikin sansanonin, sun gano mata da dama dauke da ciki, wanda hakan babban bala’i ne lura da halin da Jihar Borno ke ciki.
Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin.
Wata kididdiga da Aminiya ta samu ta nuna cewa akwai mata da suka rasa mazansu da suka haura 53,000 baya ga yara marayu 54,000, kuma watakila adadin na iya fin haka.
Jihar Adamawa
A Jihar Adamawa, wani da ya taba aiki da hukumar kare hakkin dan Adam, mai suna Malam Muhammad Sani ya ce babbar matsalar da ’yan gudun hijirar ke fuskanta ita ce ta fyade da ake yi wa yara da manyan mata a wasu lokuta.
Ya ce babban abin da ke janyo matsalar shi ne jahilci da talauci, inda yaran ke shiga lalata domin samar wa kansu abinci.
Malam Sani ya ce kuma a wasu lokuta ana kama yara kananan ana yi musu fyade a hanyarsu ta zuwa nemo itace.
Ya ce kasancewar sansanonin gudun hijirar yawanci a wajen gari suke, ya sanya akasarin gefen sansanonin daji ne.
Ya kara da cewa akwai wani lokaci da wani jami’in wani sansani ya yi wa wata ’yar shekara 13 fyade, har ta samu ciki.
“Da muka shiga maganar, sai yarinyar ta ce mu sake shi ya yi mata alkawarin zai aure ta, ita kuma son sa take,” inji shi.
Ya ce da suka bincika sai suka gano yana da mata biyu da ’ya’ya yana kuma shirin auren mata ta uku ban da ita.
Sani ya ce akwai labarin wani ma da ya yi niyyar auren wata yarinya da ba ta aure shi ba, sai ya nemi yi wa kanwarta ’yar shekara 10 fyade.
‘Labari kawai muke ji a Jihar Katsina’
A sansanin gudun hijra da ke Faskari a Jihar Katsina, wanda za a iya cewa shi ne mafi yawan ’yan gudun hijra a jihar, a ’yan kwanakin nan an rika yada jita-jitar cewa wadansu daga cikin matan da ke cikin sansanin suna aikata badala.
Da Aminiya ta ziyarci sansanin, ta ga yadda kowane aji a makarantar yake dauke da akalla mutun 40.
Malama Hassu, daya daga cikin ’yan gudun hijrar ta ce, “Gaskiya ba mu cikin matsalar da za a ce mun shiga wani hali.
“Ka ga ana ba mu kayan kwanciya da gidan sauro da tufafi da magungunna da abinci da ruwan sha da sauransu”.
Shamsiya Kogo, wadda mahara suka kashe mata miji, ta ce ta yi kimanin wata shida a wajen, amma ba ta taba fuskantar wata matsalar da za a ce har ta sanya ta fita waje don neman maza ba.
Wata mai suna Shafa ’yar garin Kafi, ta ce ta ji rade-radi da ake yi.
Ta ce, “Lokacin da na ji wadansu suna hira a kan batun badala, abin ya ban mamaki sosai.
“Na duba na ga irin yadda aka sanya masu tsaronmu, kuma a ce wai ana yin fasikanci?”
Da Aminiya tambaye ta cewa an ce wani lokaci su matan ne ke fita suna bin mazan, sai wata daga gefe ta ce, “Yanzu mace na da mijinta don ta je wajensa laifi ne? Ko shi in ya zo wajenta ya yi laifi?
“Muna da mazanmu da suka kama shaguna a cikin gari suna kwana. To shi ke nan, sai a ce wani ba zai je wajen wani ba ko don a gaisa a ga lafiyar juna?”
Kusan duk wadanda Aminiya ta tuntuba daga masu cewa sun ji ana maganar sai masu musantawa.
Aminiya ta yi kokarin ganin wadansu daga cikin mazan da aka ce suna kwana a shaguna, inda wani daga cikinsu ya ce “Ina da mata a can, kuma yanzu haka zan je in kai mata kaya ne saboda jiya ta zo ta ce tana bukatarsu.
“Na tabbata matata, ko in ce matan da ke can babu mai zuwa neman maza a waje saboda ana ba su tsaro da kulawa mai kyau”, inji shi.
Malam Aliyu Lawal shi ne Shugaban Kula da sansanin, ya ce rade-radin shashi-fadi ne kawai, inda ya ce yawan ’yan gudun hijrar ma raguwa yake yi.