A ranar 6 ga Nuwamban shekarar 1986 ce aka sallami kocin Manchester United mai suna Ron Atkinson, sannan aka maye gurbinsa da Alex Ferguson.
Sir Alex, wanda ya horar da ’yan wasan kungiyar daga shekarar zuwa shekarar 2013 ya zo kungiyar ce daga Aberdeen.
A wasansa na farko, an doke Man United da ci biyuu da nema a hannun Oxford United, sannan ya sha da kyar, inda Man U ta doke QPR da ci daya mai ban haushi a gida a ranar 22 ga Nuwamba.
A shekarar 1990, kungiyar ta so ta sallame shi, amma nasarar ta ya samu a wasan karshe na gasar Kalubale, wato FA Cup, inda Man U ta doke Crystal Palace, sai aka daga masa kafa.
Tun daga nan ya fara gyara kulob din, inda ya saya dan wasan baya, Viv Anderson daga Arsenal a matsayin dan wasan farko da ya saya.
A shekara 26 da ya yi a Manchester United, ya lashe kofuna 38, ciki har da Firimiyar Ingila 13, da Kofin Kalubale wato FA biyar da Gasar Zakarun Turai biyu da sauransu.
Ahmed Musa Ya Rabu Da Kungiyar AlNassr FC Ta Saudiyya
Ya yi ritaya da horar da ’yan wasa ne baki daya a shekarar 2013, inda a nan ma ya lashe gasar Firimiyar Ingila.
A duka, ya lashe kasi 59.67 cikin 100 na wasanninsa.
Yadda kungiyar take ta tatata tun bayan barinsa
Tun bayan barinsa kungiyar, inda ake maye gurbinsa da David Moyes, sai kungiyar ke samun kwan-gaba-kwan-baya.
David Moyes 2013-2014
A ranar 19 ga Mayun shekarar 2013 ce aka sanar da cewa David Moyes ne zai maye gurbin Sir Alex Ferguson.
A wasansa na farko ne ya lashe gasar Community Shield, inda Man U ta doke Wigan Athletic da ci biyu da nema.
Nasarar da ya samu aka yi tsammanin komai zai tafi daidai, ganin ya fara da kafar dama, amma sai kuma abubuwa suka fara tabarbarewa.
Shi ne kocin kungiyar na farko da ya fara lashe gasa a wasansa na farko, duk da cewa an riga an masa aikin a baya domin ana buga gasar ce a wasa daya tal tsakanin kungiyar da ta lashe Firimiya da wadda ta lashe Kofin Kalubale.
A lokacinsa ne Man U ta sha kashi a hannun Everton a gida a karon farko bayan shekara 21, sannan Newscastle ta doke a gida karon farko bayan shekara 41.
David Moyes wata 10 kacal ya yi yana horar da kungiyar, inda aka sallame shi kulob din tana ta 7 a tebur, maki 13 a tsakaninta da ta hudu, Arsenal.
Ya lashe gasa daya, sannan ya samu nasara a kashi 52.94 na wasanninsa.
Ryan Giggs
Bayan an sallami Moyes, sai aka ba Ryan Giggs rikon kwarya daga 22 ga Afrilun 2014 wanda ta bayyana cewa ya sha matukar wahala, inda a wasu lokuta yake kasa barci saboda tunani.
Ya samu nasara a kashi 50.00 na wasanninsa
Van Gaal 2014 zuwa 2016
A ranar 19 ga Mayun 2014 aka sanar da Van Gaal a matsayin sabon kocin Manchester United, inda ya rike Ryan Giggs a matsayin mataimakinsa domin su ci gaba da aiki.
Van Gaal ne ya sayo ’yan wasa irinsu Ander Herera da Di Maria da Luke Shaw da sauransu.
Haka shi ma sakamakon wasannin suka ta yi masa kwan-gaba-kwan-baya.
A lokacinsa Manchester United ta lashe Gasar Kalubale daya, sannan ya samu nasara a kashi 52.43 na wasanninsa.
Jose Mourinho 2016 zuwa 2018
A ranar 27 ga Mayun 2016, Jose Mourinho ya sanya hannu a kwantiragin horar da Manchester United na shekara uku.
Zuwan Mourinho, magoya bayan kungiyar sun zaci kakarsu ta yanke saka, ganin koci ne mai kwarewa da sanin yadda za a samu nasara komai wahala, sai dai wasu sun nuna rashin jin dadin zuwansa, inda suke cewa a wasu lokutan, ya cika fada da musamman manyan ’yan wasa kuma ya kan bata yanayin wasan duk kungiyar da ya je.
A ranar 7 ga Agustan shekarar, ya lashe kofinsa na karfo, inda ya doke Leicester City da ci biyu da daya a gasar FA Community Shield da ake bugawa tsakanin kungiyar da ta lashe Firimiya da wadda ta lashe ta Gasar Kalubale, wato FA.
A 18 ga Disamban 2018, Manchester United ta sallami Mourinho, bayan ya lashe wasanni bakwai kawai a cikin wasanni 17 na Firimiyar kakar.
Duk da haka a zamaninsa an dan caba, domin ya lashe gasar UEFA Europa League da League Cup da Community Shield.
Wannan ya nuna a shekara biyun da ya yi a kungiyar, ya lashe kofi uku, sannan ya samu nasarar a kashi 58.33 na wasanninsa.
Ole Gunnar Solksjaer 2018 zuwa yanzu
A ranar 19 ga Disamba ce, aka ba Solksjaer rikon kwaryar horar da Manchester United daga Molde.
Daga lokacin da aka ba shi rikon kwaryar, sai sakamakon wasannin suka gyaru, ya rike samu nasara a wasanni.
A watan Janairun 2019, shi ne ya lashe kyautar Gwarzon Kocin Firimiyar Ingila, bayan ya samu maki 10 a wasa hudu a jere; kyautar da tun da Sir Alex ya yi ritaya, ba a sake samun kocin Manchester United da ya lashe ta ba.
Sannan ya samu nasara a wasanni shida a waje a jere, nasarar da tun a shekarar 2009 rabon da a samu irinta.
Bayan ya samu nasarar a wasanni 14 cikin 19 a matsayin kocin riko, sai Manchester United ta amince da bajintarsa, inda ta ba shi damar ci gaba da jan ragamar kungiyar na dindindin bayan ya sa hannu a kwantiragin shekara uku.
Sai dai tun bayan da ya sa hannu a kwantiragin dindindin, sai abubuwa suka fara cabewa, inda shi ma abin jiya ya dawo masa.
A kakar bana, a 4 ga Oktoba, Tottenham ta yi wa Manchester United cin raba ni da yaro, inda ta lallasa da ci 6 da 1, wanda shi ne mafi girman kashi da Manchester United ta sha a Firimiyar.
Ya zuwa yanzu, ya samu nasara a wasanni 55.00, sannan bai lashe kofi ko daya ba.
Manyan ’yan wasan da Man U ta sayo bayan Sir Alex da kudinsu
Marouane Fellaini – £27.5m
Juan Mata – £37.1m
Ander Herrera – £29m
Luke Shaw – £31m
Marcos Rojo – £16m
Angel di Maria – £59.7m
Daley Blind – £13.8m
Radamel Falcao – £6m
Memphis Depay – £26.3m
Matteo Darmian – £12.7m
Morgan Schneiderlin – £25m
Bastian Schweinsteiger – £6.8m
Anthony Martial – £58m
Eric Bailly – £30m
Zlatan Ibrahimovic – kyauta
Henrikh Mkhitaryan – £26.3m
Paul Pogba – £89m
Victor Lindelof – £39m
Romelu Lukaku – £90m
Nemanja Matic – £40m
Alexis Sanchez – musaya
Diogo Dalot – £19m
Fred – £52m
Daniel James – £15m
Aaron Wan-Bissaka – £50m
Harry Maguire – £80m
Bruno Fernandes -€55m
Amad Diallo- £21.00m
Alex Telles – £15m
Edinson Cavani –Kyauta