✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kin biyan hakkin ma’aikacin KEDCO da ya rasu a bakin aiki ya jefa iyalinsa cikin kunci

Shekara uku bayan wutar lantarki ta kashe shi yana tsaka da aikin KEDCO, har yanzu kamfanin bai biya hakkokin ma'aikacin ba

Iyalin wani ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) da ya rasu yana tsaka da aiki shekaru uku da suka gabata sun shiga halin ha’ula’i saboda kin biyan sa diyya da sauran hakkokinsa.

Margayi Usman Sani mai shekaru 35 ya rasu ya bar ’ya’ya shida da mata biyu, sai dai autar ta rasu.

Yayin tattaunawarsa da Aminiya, dan uwan margayin, Ahmad Sani Dede, wanda aka fi sani da Marafan Katsina ya ce a ranar 24 ga watan Disambar 2020 ne ibtila’in ya afku, kuma KEDCO din ne suka kira shi a waya suka shaida masa cewa Usman na asibiti.

“Ni suka kira a waya lokacin ina tare da mahaifiyata, suka bukaci na je Cibiyar Kiwon lafiya ta Tarayya da ke Katsina, da naje na same su sun yi cirko-cirko, ina shiga suka nuna min sashin ba da agajin gaggawa inda dan uwana ke kwance.

“Sai na ga ashe har an rufe gawarsa da bargo. Da na bude sai na ga kansa da fuskarsa sun fashe jini na zuba, hancinsa da kunnensa duk an toshe da auduga saboda jinin da ke fita, kansa a kumbure, rigarsa kuma ta kone, kafadarsa da kirjinsa da cikinsa duka sun sabule da wuta, kugunsa da kafafunsa kuma duk sun karye.”

Marafa ya ci gaba da cewa daga nan ne suka dauki gawar margayin a motar KEDCO suka tafi gida, suka yi masa wanka aka binne shi washegari da safe.

“Bayan rasuwar margayin sai ’ya’yansa suka dawo hannuna, saboda iyayensu mata dole suka koma gidajen iyayensu saboda halin rashi da muke fama da shi.

“Ni ma’aikacin Gwamnatin Jihar Katsina ne, ina da mata da nawa ’ya’yan, ga mahaifiyarmu da ita ma nake kula da ita. Kuma saboda ba ta da lafiya, har yau ba ta ma san zancen rasuwar ba,” in ji shi.

Ya ce duk da takardun marigayin da KEDCO suka baukaci su tattaro su kai musu domin biyan hakkokinsa, kamfanin bai biya komai ba sai N200,000 da ya bayar lokacin da suka zo ta’aziyya, sai kuma albashin wata uku da suka biya bayan rasuwar Usman.

“Da albashin ya shigo, tunda na san bai kamata a yi haka ba, sai na tuntubi KEDCO, sai suka ce kada na sake na taba, domin idan na taba za su cire daga hakkokinsa da za su biya.

“To amma saboda ko kudin makarantar da za mu biya wa yaran babu, sai na kira taron ’yan uwa da matan margayin don jin yadda za a yi.

“A nan uwargidansa ta bada shawarar mu je kotu ta sahale mana amfani da kudin a biya musu. Haka aka yi kuwa, muka je Babbar Kotun Jihar Katsina ta ba mu dama.

“Daga bangarena duk takardun da KEDCO suka bukaci mu kai musu don samun hakkokin margayi Usman na kai musu, wani lokacn ma sai na yi wattani da kai musu sai kawai su yi min waya su ce na kawo, sai na tuna musu na kawo.

Binciken Aminiya dai ya gano ba iya iyalin Usman Sani ne kadai ke bin KEDCO bashin hakkokin ’yan uwansu ma’aikata da suka rasu a bakin aikin  ba – ma’aikata da iyalai da dama na kuka da hakan.

Wasu daga cikin wadanda hakan ta shafa sun bayyana mana cewa sun kai shekara bakwai suna bin hakkokin, da suka hada da na karin albashin, fansho, kudin sallama, na sauyin wurin aiki zuwa ta jihar, kudin muhalli, da sauransu.

Hakan dai ya saba wa sashi na 4 da 5 da 6 na kundin tsarin aikin kamfanin.

Abin da doka ta ce

Dokar Kwadago da kuma ta Biyan Ma’aikata Diyya ta Kasa sun bayyana cewa dole ne a biya ma’aikaci hakkokinsa da suka hada na diyyar rai, karin wa’adin aiki, da sauran hakkokin da KEDCO ta gaza biya.

Dokar Kwadago da Shugaban Kasa na wancan lokacin Goodluck Jonathan ya sanya wa hannu a shekarar 2010, an samar da ita ne domin kare hakkokin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zamna kansu, idan sun mutu ko wani tsautsayi ya same su a bakin aiki.

Sashi ma 17(1) na dokar ya tanadi biyan iyalin ma’aikacin da ya rasu yana tsaka da aiki diyya.

Sashi na 17(1)(a)(i) ya bayyana cewa duk ma’aikacin da ya mutu ya bar mata da ’ya’ya biyu zuwa sama, kamfani ko ma’aikatarsa za su dinga biyan su kashi 90 na albashinsa.

Haka kuma, sashe na 8.3.3 na kundin tsarin KEDCO ya fayyace cewa “idan ma’aikaci ya mutu ko ya samu nakasa ta dindindina bakin aiki, za a biya magadansa ninki biyar na albashinsa na shekarar.”

Wannan dai dori ne a kan gudummawar Naira 100,000 da kamfanin zai bayar kyauta ga iyalin mamacin domin hidimar jana’iza.

Sashi na 5 da na 6 na kundin ya bayyana cewa duk ma’aikacin da aka yi wa sauyin wurin aiki zuwa wata jihar za a biya shi kudin gidan da zai zauna; haka kuma za biya shi kudin hutun da ba yi ba da na sallama da sauransu idan ya ajiye aiki.

Dokokin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) suka ce ba a biya ko daya daga ciki ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Abin da kungiyar ma’aikatan ke cewa

Da yake bayyana damuwarsa kan tafiyar hawainiya da kamfanin ke yi wajen biyansu, Babban Sakataren Kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki (SSAEC), Babagana Isa ya ce KEDCO sun sha yi musu alkawarin biyan basussukan, amma har yanzu gafara sa ake, ba su ga kaho ba.

“Mun sha yin taro kan wannan matsalar amma sai alkawari babu cikawa. Mu yanzu a tsorace muke saboda ana cewa an sayar da kamfanin, ba mu san yadda za ta kasance ba game da basussukan da muke bin su,” in ji Babagana.

Sai dai mataimakin shugaban Kungiyar Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) reshen Arewa maso Yamma, Kwamred Ado Gaya, ya ce sabon shugaban KEDCO da aka nada Ahmad Dangana ya fara rage bashin fansho da ma’aikata ke  bin su.

“Duk da ba mu san nawa ko su wa aka biya ba, mun samu labarin an biya wadansu ma’aikatan. Amma sauran hakkoki da diyya babu wanda aka biya tukunna.

“Amma a matsayinmu na kungiya za mu tabbatar sun fara a taron nan gaba da za mu yi da jagororin KEDCO,” in ji shi.

Mun fara biya —KEDCO

A nasa martanin, kakakin KEDCO Sani Bala Sani, ya bayyanawa Aminiya cewa kamfanin yana sane da wadannan basussukan kuma tuni ya fara daukar matakan rage su.

“Wadannan matsalolin ne da muka gada kuma ana kan gudanara da bincike a kansu.

“Wanann ne dalilin da ya sanya aka sauya shugabancin kamfanin a shekarar 2022 bayan ya koma hannun Bankin Fidelity. Kuma ana sauyin muka fara daukar matakan rage wadannaan basussuka.

“Abin da muka tsara shi ne duk wata muna ware wani adadi na ma’aikatan da za mu biya saboda ba mu da kudin da za mu biya kowa a lokaci daya.

“Za ta yi wu su wadanda kike magana a kai ba a zo kansu ba ne. Amma dai wannan shi ne matakin da muka fara dauka a yanzu,” in ji jami’in kamfanin.

 

Cibiyar Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism (WSCIJ) ce ta tallafa wa wannan binciken ta hannun Stallion Times bisa haɗin gwiwar Media Engagement for Development Inclusivity and Accountability Project (CMEDIA) wanda Gidauniyar MacArthur ta dauki nauyi.