A yau za mu duba wani batu na dokoki wadanda musamman mu ma’aikatan lafiya muke takewa na rashin ba da hakkoki da yada sirrin marasa lafiya ga jama’a, a wasu lokuta ma har ga gidajen watsa labarai ba tare da yardarsu ko amincewarsu ba.
Mu ma muna da namu hakkokin a kan marasa lafiya wadanda za a yi maganarsu a mako mai zuwa.
- Ana shirin yanke wutar Fadar Shugaban Kasa saboda bashin fiye da N300m
- Direbobin dakon man fetur sun dakatar da yajin aiki
Hakkin marasa lafiya ne mu tsare musu sirrinsu. Tsare sirrin bayanan maras lafiya wajibi ne ga kowane ma’aikacin lafiya.
Akwai dokoki da hukunce-hukunce masu tsauri idan aka samu wani ma’aikacin lafiya da keta haddin bayanan maras lafiya.
Ban da bayanan rashin lafiya, tsare sirrin bayanan maras lafiya ya shafi har da wasu bayanai masu nuni da ko shi wane ne, kamar lambar katin dan kasa ko shekaru ko adireshi da lambobin waya.
Maras lafiya na da hakkin ya kai duk wanda ya keta dokar tsare sirrinsa ga hukuma domin a ba shi hakkinsa.
Dole a fayyace wa maras lafiya dukkan bayanan da yake bukata a game da rashin lafiyarsa, sabanin yadda akan yi biris da marasa lafiya idan sun yi tambaya.
Kuma ba za a ba kowa bayanan maras lafiya ba komai kusancinsu da maras lafiyan, sai da izinin maras lafiya.
Ba za a ba wa kowane ma’aikaci a asibiti wasu bayanai na maras lafiya ba, sai mai lura da shi kai tsaye, kamar likitoci da nas-nas da ke kula da shi.
Idan aka ga wani ma’aikaci yana keta wadannan dokoki dole ne shi ma a kai shi ga hukumomin asibiti domin daukar mataki.
Wadannan dokoki sun shafi kowane ma’aikaci a asibitin tun daga kan shugaba har zuwa masu shara da masu gadi.
Maras lafiya kuma yana da zabi a kan wanda yake so ya kula da shi.
Yana iya tambayar sunansa ko sunanta a fada masa Maras lafiya yana da damar canzawa ko kara neman shawarar wani ma’aikacin lafiyar idan yana son bayanai gamsassu.
Kada a sa mara lafiya cikin binciken aikin lafiya ba tare da sanin sa ba. Idan ma ya ba da goyon baya yana da damar ya fita a duk lokacin da yake so.
Maras lafiya yana da damar a duba shi, a ba shi magani a ko’ina a kasar nan ko ma a ko’ina a duniya ba tare da wani bambancin launin fata ko yare ko addini ko jinsi ba.
Iyaye suna da damar su san ko me ake yi wa ‘ya’yansu na magani idan suka kawo su asibiti ko wane magani ko aiki za a musu. Haka kuma suna da ta cewa a kan magungunan da ake ba yaran.