Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram tara, ciki har da ƙwararren mai haɗa wa ƙungiyar bama-bamai, Amirul Bumma a wani samame da suka kai a dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun kai farmakin ne a Ƙaramar Hukumar Bama, ƙarƙashin rundunar Operation Desert Sanity 4, bayan samun bayanan sirri.
Boko Haram sun yi ƙoƙarin tsayawa da su fafata, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su.
Bayan kammala artabun, mayaƙan sun dawo wajen da gadajen asibiti domin kwashe waɗanda suka jikkata, wanda hakan ke nuna girman asarar da suka yi.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai babban jagoran Boko Haram, Amirul Bumma tare da wasu manyan kwamandoji kamar Bakura Ghana, Awari, Malam Kalli, Malam Usman Bula Kagoye, da Ibrahim Bula Abu Asma’u.
Hakazalika, sun kashe wasu biyu da ba a tantance sunansu ba.
Har ila yau, sojojin sun ƙwato muggan makamai daga hannunsu.
A wani yunƙuri na ramuwar gayya, Boko Haram sun dasa bama-bamai a hanyar da sojojin suke bi, amma dakarun sun gano nufinsu tare da cire bama-bamai.
Babban Kwamandan runduna ta 7, Manjo Janar Abubakar Haruna, ya yababwa sojojin bisa wannan gagarumar nasara, da suka samu.
Ya jaddada cewar za su ci gaba da yaƙi da ta’addanci har sai an kawo ƙarshensa a Najeriya.