Shirin gwamnatin Kano na gina gadar sama a Kofar Dan Agundi ya bar baya da kura, inda ake ta musayar ra’yai.
Gwamnain Kano na shirin gidan gadar a kan kudi kimanin Naira biliyan 16, daga asusun jiha da na kananan hukumomi.
Wasu ke ganin kudin aikin ya yi yawa, wasu kuma na cewa ingana bangaren ilimi da wasu bangarori ne suka fi muhimmani ba gina gadar ba.
A kan haka ne Aminiyaa a nemi jin ra’ayain Kanawa kan wannan al’amari, ga kuma abin da suka bayayana mana a Facebook.
- Ilimi Kanawa su ke bukata ba gadar sama ba —Kwankwaso
- Kotun Koli ta sanya lokacin yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Kano
Malama Danzabuwa ya ce, WWallahi muna so” Abubakar Bello kuma ya ce, “Hakan duk cikin aikin ne”
Daddee Gamoji, ya ce, gina gadar “Ba shi da amfani wallahi, in dai da kudin local government na jihar kano za a yi. Kuma rogowar kananan hukumomin da suke cikin kauye kuma fa?”
A nasa bangaren, Haruna DjBombo na ganin, “a shiga kauyuka a gani musu hanyoyi da rijiyoyin birtsatsai,” zai fi.
Amma Habib Kanana ya ce, “An faninsu daya ne da wadanda aka gina a baya, kada a yi siyasa da cigaban birni. Ko an tafi karkara an raya su ba zama ake yi a karkaran ba…saboda haka su za a gina wa Gadar Dan agundi.”
Haka shi ma, Abubakar Garba, ya ce, gina gadar saman “Yana da muhimmanci duba da yadda ake cinkoso a wajen”
“Duk mai bin hanyar ya san akwai cinkoson ababen hawa,” in ji shi kuma Usman Danbazau
Shi ma El Ameen Aliyu Isah, ya ce, “Muna so kawai dai kudin ya fi kamata a sa shi a wani wajen.”
Amma kuma Jibril Mohd Sani na da ra’a in “Wannan rashin adalci ne kawai ake nuna wa mutanen karkara.”
Shi kuma Comrd Muhammad Umar cewa ya yi, “Haba yayi gefe da yawa. Ku zo Bichi muna da bukata.”
Bashir Ibrahim Haruna ya ce, “A matsayina na masoyin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba na goyon bayan gina gadar sama a Kofar Dan Agundi. In dai don talaka ake yin mulki to a taimaki kananan hukumomi da ayyukan raya kasa, hakan zai rage radadin talauci da ake fama da shi a Jahar Kano.”
Ku mene ne ra’ayinku.