Gaba daya mutane sun kaurace wa akalla kananan hukumomi uku na Jihar Borno sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdulkareem Lawan, ya ce sojoji da farar hula sun kaurace wa Kananan Hukumomin Guzamala, Marte da Abadam, yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da girke karin sojoji a Arewacin jihar domin masu gudun hijira su samu su koma garuruwansu.
“Akwai al’ummomi kusan 170 a Guzamala amma yanzu babu ko mutun daya a cikinta, babu soja ko wani jami’in tsaro daya a fadin yankin Guzamala.
“A Abadam babu ragowar farar hula; akwai sansanin soja a hedikwatarta (Malam Fatori) da ke gadi, amma babu farar hula ko mutum daya.
“Yawancin mutane Abadam sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar ko garin Monguno. Haka abin yake ma a Marte”.
Da yake karabar bakuncin matasan Guzamala a Maiduguri, Shugaban Majalisar ya ce dole ne duniya ta halin da ake ciki a kuma dauki mataki kan yanayin na Guzamala, Marte da Abadam.
– Sojoji ma ba su tsira ba –
Bayanan nasa na zuwa ne haka ne jim kadan bayan bullar rahoton mutuwar soja tara a wani sansani da mayakan Boko Haram masu biyayya ga kungiyar ISWAP suka kai musu a Magumeri da Kukawa.
Dauki ba dadin ya yi sanadiyyar mutuwar adadin mayakan kungiyar da ba a kai ga tantancewa ba, duk da cewa wasu majiyoyin tsaro da kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito na cewa sojoji kashe 20 daga cikin maharan.
Babban Jami’in Yada Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ki ce wa wakilinmu uffan kan rahoton.
– Yadda ISWAP da sojoji suka yi dauki ba dadi –
Kazamar fada ta kaure tsakanin sojoji da mayakan ISWAP a ranar Talata a lokacin da mayakan suka yi yunkurin kwace wani sansanin soja a Magumeri.
Mayakan sun kashe sojoji tara a artabun kafin daga bisani wata tawagar dakaru na musamman daga Maiduguri su yi musu kofar rago su kashe akalla 20 daga cikin mayakan.
Maharan a cikin motocin yaki 10 sun yi wa sansanin tsinke ne da la’asar, inda suka kai ga lalata wani bangare da sansanin sojan.
“Sun kona motoci uku a sansanin sojan da suka hadar da mota mai sulki da ta hakar rami da sojojin ke amfani da ita domin yin shigen yaki”, inji wa wani dan banga a Magumeri, Mohammed Ali.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun “kon manyan motoci guda biyar da motar da bam ba ya fasawa daya sannan suka sace makamai daga sansanin sojin.
“Sun kuma lalata kadarorin gwamnati. ISWAP ta yi kacakaca da sansanin sojin.
“Sun lalata motocin yaki biyu da motar gina rami. An lalata Hilux daya na ISWAP amma kuma sun dauke guda daya daga sansanin cike da kayan abincin da aka kaw”, inji wata majiya.
Magumeri ya sa hama da hare-haren kungiyar a baya-bayan nan, inda mayakan kungiyar suka kona babban asibitin garin da sakatariyar karamar hukuma baya ga yi wa ‘yan garin fashi da makami.
A wani kaulin kuma ‘yan ta’adda sun kashe wasu sojoji a wani hari da suka kai garin Baga a Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno, mai makwabataka da Tabkin Chadi.
Dauki ba dadin na ranar Alhamis ya faru ne da la’asar a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai wa wani sansanin soja farmaki a garin Gubio.
Ko da yake babu cikakken bayani game da irin asarar da aka yi a harin na Gubio.