Jama’a da dama a Jihar Kano sun koka kan yajin aikin da matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da A Daidaita Sahu suka shiga.
A ranar Litinin ne matukan na A Daidaita Sahu suka fara yajin aiki kan matakin gwamnatin jihar na wajabta musu sake sabunta rajistar lambar baburan.
- Yajin aiki: ’Yan Adaidaita Sahu sun tafka asarar N300m a yini daya a Kano
- AFCON 2021: Wasan Najeriya da Masar (kai-tsaye)
Yajin aikin ya kawo tsaiko ga ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni da ‘yan kasuwa, ’yan makaranta da sauran al’umma.
A kan haka ne Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta soke jarawaba da dalibanta za su zana a ranar Litinin.
Aminiya ta samu tattaunawa da wasu mutane da suke jiran abun hawa a Kano, inda kowannensu ya bayyana halin da ya tsinci kansa.
Kabiru Garba, dan kasuwa ne, ya shaida wa Aminiya cewa, “Ni ban san sun shiga yajin aiki ba, sai da na fito na ga mutane sun yi cirko-cirko, da kyar na samu wani ya rage min hanya zuwa kasuwa.”
Auwalu Usman, wani ma’aikacin gwamnati ne a Kano, ya ce, “Gaskiya jiya da yau ban samu zuwa aiki ba, sai waya na yi ofis na sanar da su halin da ake ciki, yanzu ma na fito neman wani abu ne shi ne dalilin da ya sa na fito.”
Wata daliba da ta bukaci a sakaya sunanta kuma cewa ta yi, “Da safe na samu wani dan unguwarmu ya rage min hanya zuwa makaranta, amma yanzu tun ranar nake tafiya a kafa ga shi na gaji, saboda babu masu A Daidaita.”
Wani magidanci mai suna Mubarak Saulawa, ya ce, “Magana ta Allah wannan yajin aikin ya tsayar da abubuwa da dama, ya kamata gwamnati da kungiyar masu A Daidaita Sahu su zauna don yin sulhu.”
An kai mu makura —dan A Daidaita Sahu
Wani matukin A Daidaita Sahu mai suna Saleh Kabiru shi ma ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin.
“An kai mu bango ne shi yasa muka shiga yajin aikin. Kullum sai mun bayar da harajin N120, a bara ma sai da irin haka ta faru.
“Rayuwa ta yi tsada amma gwamnati ba ta tausaya mana ga shi ’yan KAROTA sun takura mana sosai.”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar KAROTA ta Kano, Baffa Babba DanAgundi, wanda ya shaida mata cewa gwamnati na kokarin kawo karshen yajin aikin.