✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda kananan yara suka rasu yayin wasa a cikin fada

Wasu kananan yara biyu sun rasu yayin da suke wasa a cikin wata motar da aka yi watsi da ita a garin Kuje, Birnin Tarayya,…

Wasu kananan yara biyu sun rasu yayin da suke wasa a cikin wata motar da aka yi watsi da ita a garin Kuje, Birnin Tarayya, Abuja.

Yaran da suka hada da mai shekara takwas da kuma shekara hudu, sun gamu da ajalinsu ne yayin da motar da suke wasa a ciki ta rufe da su, har numfashinsu ya dauke.

Wani mazaunin Kuje, Yakubu Usman, ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’ar da ta gabata, bayan saukowa daga Salla Juma’a bayan mahaifiyarsu ta sanar cewa sun bace.

Ya ce mahaifin yaran ma’aikacin fadar Gomon Kuje ne, Alhaji Haruna Tanko Jirbrin, inda yaran ke wasa a cikin motar da ke a farfajiyar gidan.

“Tun misalin karfe 2 na ranar aka sanar cewa sun bata, sai misalin karfe 7 na yamma aka gano gawarsu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a fadar,” inji shi.

Nan take aka garzaya da su asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu, aka kuma binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sakataren Gomo na Kuje, Usman Mohammed Bako, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho.

Ya ce yaran na wasa ne a cikin harabar fadar bayan sallar Juma’a, lokacin da suka yi batan dabo kuma aka tsinci gawarsu a cikin motar da misalin karfe 7 na yamma.

Masu ta’aziyya ciki har da manyan ’yan siyasa ke cincirindo a fadar don yi wa Gomo na Kuje, ta’aziyar rasuwar yaran biyu.