A wannan Juma’ar ce mahukunta Kwallon Kafar Turai wato UEFA suka fitar da jadawalin matakin ’yan takwas din karshe na Gasar Zakarun Turai ta Champions League.
A kunshin jadawalin, Real Madrid za ta fafata da Chelsea a matakin daf da na kusa da na karshe a babbar gasar Turan ta bana.
- An yi garkuwa da dan takarar mataimakin gwamna
- Yadda sojoji suka gudanar da Musabakar Al-Kur’ani a Borno
Ko a kakar da ta gabata, kungiyoyin sun hadu a irin wannan matakin inda Real Madrid ta samu nasara a kan Chelsea.
A bana dai Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.
Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.
Mai rike da Firimiyar Ingila, Manchester City za ta kara da Bayern Munich, mai Champions League shida.
Inter Milan za ta yi tata burza da Benfica, mai rike da kofin Serie A, inda ita kuma AC Milan za ta fuskanci Napoli.
Idan Chelsea da Manchester City su kai zagayen gaba, ke nan za su iya haduwa a daf da karshe, wata kila AC Milan ko Napoli ta fuskanci Inter Milan ko Benfica a daya wasan daf da karshe.
Jadawalin kwata final a Champions League
- Inter Milan da Benfica
- Real Madrid da Chelsea
- Manchester City da Bayern Munich
- AC Milan da Napoli
Wasannin daf da na kusa da na karshe
Ranar 11 ga watan Afirilun 2023
Inter Milan da Benfica
Real Madrid da Chelsea
Ranar 12 ga watan Afirilun 2023
Manchester City da Bayern Munich
AC Milan da Napoli
Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Chelsea a Santiago Bernabeu a wasan farko ranar 11 ga watan Afirilu.
Sannan Chelsea ta karbi bakuncin wasa na biyu a Stamford Bridge ranar 19 ga watan Afirilu.
Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce mai rike da na bara kuma na 14 jimilla.
Za a fara buga wasannin farko ranar Talata 11 da kuma Laraba 12 ga watan Afirilu, sannan a yi wasa na biyu tsakanin 18 da kuma 19 ga watan Afirilu.
Za a fara wasan farko a daf da karshe daga ranar 9 da 10 ga watan Mayu, sannan a buga zagaye na biyu ranar 16 da 17 ga watan Mayu.
Za a buga wasan karshe ranar Asabar 10 ga watan Yunin 2023 a Istanbul a filin wasa Ataturk Olympic Stadium.