Daya daga cikin wadanda suka shaida harin da aka kai kan jirgin kasa da ke tafiya Abuja daga Kaduna a ranar Litinin da daddare, ya ce sojoji da ’yan bindiga sun yi musayar wuta ta akalla sa’o’i biyu yayin faruwar lamarin.
A cewar ganau din wanda ya bukaci a sakaya sunansa, mutum shida ciki har da masu sayar da abinci sun rasa rayukansu a harin, duk da cewa Aminiya ba ta iya samun tabbaci kan hakan a hukumance ba.
- An dakatar da sufurin jirgin kasa na tsakanin Kaduna da Abuja
- Taliban ta haramta wa mata shiga jirgin sama, ta hana maza marasa gemu shiga ofis
Bayanai sun ce jirgin ya kauce daga kan hanyarsa bayan fashewar wani abu a kan layin dogon, lamarin da ya bai wa maharan damar shiga cikin jirgin har suka yi awon gaba da wani adadi na fasinjoji.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, an garzaya da wadanda suka jikkata da kuma gawawwakin wadanda suka rasu zuwa Asibitin 44 Reference da ke Jihar Kaduna.
Gwamnatin Kaduna ta umarci dukkan manyan asibitoci da su yi jinyar wadanda abin ya shafa, tana mai shan alwashin biyan kudin da dawainiyarsu za ta ci.
Wasu rahotannin kuma sun ce an harbe Muhammad Amin Mahmood, wanda ya nemi kujerar Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Kasa shiyyar Arewa maso Yamma a yayin Babban Taron Jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Asabar a Abuja.
Yadda lamarin ya faru
Wani fasinja mai Musa Usman, ya ce ’yan bindigar ta karfin tsiya suka shiga taragon da ake ware wa mutane na musamman da kuma taragon jirgin mai lamba 17, inda suka kashe na kashewa suka debi na diba.
“Sun yi ta harbe-harbe wanda hakan ce ta sanya wadanda ba su farga da abin da ke faruwa ba harsashin bindiga ya same su.”
Sai dai ya ce wata tawagar sojoji da ta kawo dauki da misalin karfe 10.00 na dare ce ta sanya ’yan bindigar suka tsere tare da fasinjojin da suka diba.
Haka kuma, wani fasinja ya ce akwai wani tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara da aka harba a kafufunsa biyu yayin harin.
“Mun ji mutane da dama suna cewa ai Tsohon Mataimakin Gwamna ne amma ba zan iya tabbatar da ko wanne ne daga cikin tsoffin mataimakan gwamnonin ba,” inji shi.
Sai dai Aminiya ta samu tabbacin cewa, Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad, shi ne tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara da lamarin ya rutsa da shi.
Yusuf Idris, wani mai magana da yawun tsohon mataimakin gwamnan ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da wakilinmu.
Ya ce a halin yanzu Sarkin Malaman Gusau din yana samun kulawa a wani asibiti a Kaduna, saboda haka babu wani abun daga hankali.