A farkon kakar bana ce Kungiyar Manchester City ta dauko dan wasan gaba, Erling Haaland daga Kungiyar Dortmund ta Jamus.
Yadda dan wasan ya yi kaca-kaca da Kungiyar Manchester United a makon jiya ne ya sa magoya bayan kungiyar suke cewa lallai kakarsu ta yanke saka, domin matsalarsu ta rashin zura kwallaye ta kare, bayan sun yagalgala Manchester United da ci 6-3.
- Buhari zai karrama Sheikh Rijiyar Lemo da lambar girmamawa ta OON
- Sojoji sun kashe Ali Dogo da ‘yan bindiga 30 a Kaduna
Zuwansa kungiyar ke da wuya, a wasan farko da Manchester City ta buga, kungiyar ta doke Kungiyar West Ham da ci 2-0, inda matashin dan wasan gaban ya zura kwallon biyu.
Kafin zuwansa Manchester City, masu sharhi sun rika cewa ba zai yi daukar nauyin kungiyar ba, musamman duba da girmanta, inda wasu kuma suke cewa ai gasar Firimiyar Ingila za ta yi masa girma.
Haka kuma magoya bayan kungiyar suka fara shiga zullumi bayan dan wasan ya gaza tabuka komai a wasansa na farko, inda Kungiyar Liverpool ta doke Manchester City din a wasan cin Kofin Community Shield, wanda hakan ya sa wasu musamman ’yan adawar kungiyar suka fara cewa an yi sayen tumun-dare ne.
A tarihin Kungiyar Man City, Sergio Aguero ne kawai ya taba zura kwallo biyu a wasan farko na kungiyar, sai Haaland da ya biyo baya.
Yadda Haaland ya canja Manchester City
Kungiyar Manchester City ta dade tana jan zarenta a gasar Firimiya ta Ingila, da duniyar kwallon kafa.
Sai dai kungiyar ba gasar Firimiya ta Ingila ba ce a gabanta, domin ta lashe da dama a cikin shekaru kadan, gasar Zakarun Turai ce ta sa a gaba.
Ko a kakar bara, kungiyar ta nuna bajinta sosai, sai dai masu sharhi a kan harkokin kwallon kafa sun bayyana rashin tsayayye kuma kwararren dan wasan gaba a matsayin matsalar da kungiyar ke fuskanta.
A kakar bana, kungiyar ta sayar da zaratan ’yan wasan gabanta guda biyu: Raheem Sterling ga Kungiyar Chelsea da Gabriel Jesus da ya koma Kungiyar Arsenal.
Hakan ya sa kocin Kungiyar, Pep Guardiola ya dauko Haaland, wanda ake yi wa kallon matashin dan wasan gaba mafi kwazo a yanzu, inda yake kafada-dakafada da dan wasan Kungiyar PSG, Mbappe.
A kakar bara, dan wasan ya zura kwallo 62 a wasa 67 da ya buga a Kungiyar Dortmund ta kasar Jamus, wanda hakan ke nuna bajintarsa.
Matashin dan wasa ne da ya kware wajen jefa kwallo a raga, sannan Kungiyar Man City a karkashin jagorancin Koci Pep Guardiola tana nuna kwarewa wajen taka leda da nemo hanyoyin zura kwallaye, amma a lokuta da dama a barnatar.
Shin da dauko Haaland za a yi cewa matsalarsu ta kare?
Hakan magoya bayan kungiyar suke tunani, musamman ganin yadda dan wasan ya fara da kafar dama, inda yake ta zura kwallo ba kakkautawa.
Dan wasan mai shekara 22, ya zura kwallo 15 a gasar Firimiya ta Ingila kadai, sannan yana da kwallo 18 jimilla a wasanni 12 da ya buga tun zuwansa kungiyar ta Manchester City a farkon kakar bana.
Daga cikin kwallaye da ya zura, akwai kwallo uku rigis da ya zura sau uku a jere, inda ya zura kwallo uku a ragar Crystal Palace da Nottingham Forest da kuma Manchester United a makon shekaran jiya.
Hasashen kwallayen da zai iya zurawa a bana A tarihin gasar Firimiya ta Ingila, dan wasan gaba na Liverpool, Mohammed Salah ya kare da kwallaye mafiya yawa, inda ya lashe kambun Takalmin Zinare na wanda ya fi zura kwallaye da kwallo 38 a kakar 2018.
Sai dai yadda Haaland ya zura kwallo 14 a wasa takwas kacal, ana hasashen zai iya ninka wannan adadin na Salah.
A wani hasashe da wasu masu nazarin harkokin wasan kwallon kafa suka yi a kafar labarai ta Skysport, sun ce idan har Haaland ya ci gaba da bajinta haka, zai iya zura kwallo 67 a gasar Firimiya ta Ingila kawai.
Haka kuma hasashen ya nuna cewa idan Haaland ya buga dukan wasannin kungiyar a kakar bana, zai iya zura kwallo 71.
Hasashen kuma ya nuna cewa idan Manchester City ta kai wasan karshe a duk gasannin da take ciki, dan wasan zai iya karewa da kwallo 95, sannan zai iya zura kwallo 102 idan ya buga dukan wasannin kungiyar ba tare da an canja shi ba.