Harkar kiwon kaji a Jihar Filato tana da karfi da tasiri wajen samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arziki.
Sannan kwan da ake samu daga jihar da tsakiyar Najeriya na cikin mafi kyau daga sauran kwayayen kaji da ake samu a wasu sassan kasar nan.
Baya ga haka, sana’ar kiwon kaji a jihar na daya daga cikin sana’o’in da suke samar wa mutane aikin yi, kasancewar jihar na da wuraren da ake kiwon kaji sama da 4,000, kuma a kowane wuri ana samun akalla ma’aikata 10 ko 20.
Sai dai kamar yadda ba a rasawa kowace sana’a na da matsaloli nan da can, haka masu kiwon kaji a jihar suke fama da wasu matsaloli da suka tilasta wa wasu musu kiwon kaji rufe gidajen gonarsu, wasu suka bar sana’ar baki daya.
Wadanda suka ci gaba kuma da kyar suke mayar da abin da suka zuba.
Muhimmai daga cikin matsalolin su ne tsadar abincin kaji da ta ’yan tsaki da magunguna da rashin tsayayyiyar kasuwar kwai da kajin.
Kafin wannan yanayi, masu kiwon sun sha fama da cutar murar tsuntsaye da ta haifar da mutuwar kaji da yawa.
Haka a hunturun bara sun yi fama da mutuwar kajin. Matsala ta baya-bayan nan ita ce karancin kudi sakamakon sauya fasalin takardar Naira 1,000 da 500 da 200, a kasa baki daya.
Wannan matsalar ta ce ta sa Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Kasa reshen Jihar Filato, Mista Johnson Bagudu ya koka game da illar da sauya kudin na Bankin CBN ta haifar ga mutanen jihar, musamman ’ya’yan kungiyar da kuma sana’ar kiwon kaji a jihar baki daya.
Bagudu ya ce, sauya takardun kudin ya karya farashin kwan kaji, wanda hakan ya haifar musu da mummunar asara.
Saboda sai an sayar ake sayen abincin kajin da biyan ma’aikata da gudanar da aikace-aikacen gidan gonar baki daya.
Rashin cinikin ya sa kasuwar kwan ta cushe hakan ya sa farashinsa ya fadi warwas.
Domin kuwa ana sayar da kiret din kwai a kan 1,000 maimakon 2,100 da ake sayarwa a baya.
Ya ce, da yawa daga cikin masu kiwon sun kasa sayar da kwan nasu saboda rashin kasuwa.
Wasu kuma sun rika sayarwa bashi, wasu kuma ta hanyar taransfa zuwa asusun banki, wanda hakan ya haifar da matsaloli da yawa ga masu kiwon kajin, wadanda suke bukatar kudi hannu domin ci gaba da gudanar da gidajen kajinsu.
Shugaban ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kawo wa ’ya’yan kungiyar dauki ta hanyar saye kwan da ke kasuwa, wanda hakan ya sa farshinsa ya fadi warwas.
An yi katarin amsa wannan kira daga gwamnatin, inda Gwamnan Jihar Simon Lalong bayan ya yi alhinin faduwar farshin kwan da rashin kudin da ya haifar da matsaloli ga masu kiwon da kajin da kuma sana’ar, sai ya ce gwamnati za ta saye kwan da ke hannun kungiyar, ya kuma umarci a rarraba shi ga gidanjen marayu da na gyaran hali da makarantu da kuma asibitocin jihar.
Cikin hanzari kungiyar ta hada kan ’ya’yanta ta kuma tattaro duk kwan da ke wurinsu tare da mika wa gwamnati ta hannun hukumar da ta dace.
Bagudu ya kiyasta adadin kudin kwan da gwamnatin ta saya ya kai na Naira miliyan 10.
Sannan ya ce, duk da cewa gwamnatin ba ta kai ga biyan su ba, amma hakan ya sa farshin kwan ya daidaita a kasuwa.
Mutane da yawa sun yi murna da wannan dauki da gwamnati ta kai wa masu kiwon kajin ta hanyar saye kwan nasu.
Mista Yilkes Zumunci Bitrus wani tsohon Manajan Gonar ECWA da ke Jos, ya ce, wannan mataki da gwamnatin ta dauka ba karamin taimaka wa harkar kiwon kaji ya yi ba, duba da muhimmancin harkar ga ci-gaban kasa da samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arziki.
Tasirin daukin gwamnatin ga masu kiwon kajin
Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna farashin kireti din kwai yanzu a Jihar FIlato ya haura 1,000.
A cikin garin Jos da wasu wuraren, farashin ya kai 1,200 zuwa 1,300.
Kodayake an danganta tashin farashin ga azumin watan Ramadan da Musulmi ke yi, sakamakon bukatar kwan da ake yi a yayin shan ruwa.
Amma rashin yawansa a kasuwanni saboda saye shi da gwamntin ta yi ya taimaka.
Haka kuma ya hana harkar kiwon kaji a jihar durkushewa saboda kwan na iya lalacewa saboda ba ya jure ajiya, kuma rashin kudi ya sa a baya masu kiwon gaza ciyar da kajinsu.