✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta yi ajalin mutum 4 a Filato

Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol.

Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol.

Galibin waɗanda ake zargi sun harbu da cutar an killace su a cibiyoyin lafiya a matakin farko daban-daban da kuma Asibitin Cottage inda suke samun kulawar gaggawa.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bokkos, Mista Amalau Samuel Amalau wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna aiki tare da mahukuntan asibitin domin daƙile ƙalubalen

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ke fama da rashin lafiyar sun fara samun sauƙi yayin da tuni an sallami wasu daga asibiti.

Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya gargaɗi mazauna da su riƙa taka-tsan-tsan wajen kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta domin kaucewa kamuwa da cutar musamman tsaftace jiki, muhalli da kuma uwa-uba abinci.