✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato

Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zaune a Jihar Filato.

Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai  wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato.

Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a ƙaramar hukumar ta Mangu.

Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin a wannan makon tsakanin yan kabilar Mwaghavul da Fulani.

Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar Mangu a ranar Litinin da Talata, sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da ake kyautata zaton sun fara ne yayin da mutane ke aikin haƙar ma’adinai a yankin da ke da arzikin Tin, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ta ruwaito Emmanuel Bala yana cewa, “Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zaune a Jihar Filato — waɗanda mafi yawansu Kiristoci ne — kan rikicin mallakar fili da albarkatun ƙasa.”.

Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa a yankin sau da yawa na da nasaba da bambancin ƙabila da addini, wanda ke haifar da hare-haren ramuwar gayya marasa kakkautawa.

“Watanni da suka wuce, wasu mazauna yankin na aikin haƙar ma’adinai, sai aka kai musu hari da adduna, kodayake babu wanda ya mutu a harin farko.

“Amma bayan jerin ramuwar gayya da martani, an kai hare-hare uku a ranar Litinin da Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20,” in ji Bala.

Wani jami’in Red Cross ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu cikin sa’o’i 24 a harin Chinchin, yana mai cewa adadinsu na iya kai wa 21.