✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta cinye kauye mai shekara 400 a China

Da kyar bukkoki hudu suka tsira a gobarar kauyen Wengding.

Gobara ta babbake wani kauye mai shekara 400 da kafuwa, inda ta cinye bukkoki fiye da 100 a kasar China.

Bukkoki 101 suka kone kurmus a gobarar ta safiyar Litinin, ta bar bukkoki hudu rak a kauyen na Wengding inda kabilar Wa marasa rinjaye a kasar ke zama.

 

Gidan talabijin na kasar China ya ruwaito cewa yawancin bukkokin an yi su ne daga karmami da itatuwa a kauyen na Wengding mai nisan kilomita 30 daga iyakan kasar China da Myanmar.

Al’ummar kabilar Wa na kasar China na zaune ne a yankunan Ximeng, Cangyuan da kuma Menglian da ke lardin Yunnan na kasar kuma tana da yawan al’umma sama da 400,000.

Sai dai hukumomin China sun ce iyalai 12 ke ci gaba da zama a cikin bukkokin da gobara ya ritsa da su.

Sun ce ba a samu asarar rai gobarar ba, sai dai mutum daya ya samu rauni.

Yawancin ’yan kauyen sun koma da zama a cikin gine-ginen siminti da ke da daura da bukkokin da suka yi gobara.

Ana ganin kauyen a matsayin matsugunin al’ummar  ’yan gargajiya dadewa a kasar China.