✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Giya ta Kashe Sama da Mutum 100 a Indiya

Mutum sama da 100 ne suka gamu da ajalinsu a kasar Indiya bayan sun sha gurbataciyyar barasa a yankin arewacin kasar. Mutanen da suka mutu…

Mutum sama da 100 ne suka gamu da ajalinsu a kasar Indiya bayan sun sha gurbataciyyar barasa a yankin arewacin kasar.

Mutanen da suka mutu bayan sun kwankwadi barasar sun hada da talakawa manoma da leburori a yankin Punjab, inda suka yi ta rashin lafiya kafin daga bisani su ce ga garinku nan.

An kuma bayar da rahoton mutuwar kashi na farko na mutanen ne ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, wadanda adadinsu ya kai mutum 21.

A cewar wani babban jami’i a kasar ta India, Kulwant Singh, mutum takwas sun mutu ne a gundumar Tarn Taran a cikin kwanaki biyar da suka gabata, kana ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 25 a gundumomin Amritsar da Batala.

Zuwa yanzu ‘yan sandan  kasar sun kama mutum 30 da ake zargi da hannu a samar da gurbataciyyar barasar da tayi sanadiyar mutuwar mutanen, sun kuma rufe wurare da dama inda ake sayar da barasa.

Sun kuma kwace gurbataciyyar barasar da ta haura lita dubu.

Binciken farko ya tabbatar da cewa barasar na dauke da sinadarin ‘methanol’ wanda ka iya makantarwa  ko hallaka wanda ya kwankwadi barasar dayawa.

Mahukunta sun dakatar da wasu jami’ai bakwai da ke da alhakin kula da masana’antun barasa, hakazalika sun dakatar da karin wasu ‘yan sanda shida.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da jam’iyun  adawa na kasar ke zargin jam’iya mai mulki da bai wa masana’antun barasa marasa inganci mafaka.

Bayanan da mahukunta a kasar suka tattaro sun nuna cewa a duk shekara, mutum 1,000 na mutuwa sakamakon shan gurbataciyyar barasa a Indiya.

Gurbataciyyar barasar, wacce sau tari ake sanya mata miyagun sinadaran masana’antu wadanda ba a yi su domin sha ba, ana samar da ita ne ta barauniyar hanya.

A shekarar da ta gabata ma mutum 151 da ke leburancin aikin gona ne suka rasa rayukan su bayan da suka sha gurbataciyyar barasar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito.