✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gidajen rediyo ke yawaita a Kano

Akwai gidajen rediyo 40 da akasari ba su biyan ma'aikata albashi.

Rediyo na daga cikin kafafen watsa labarai da ake isar da sakonni ga al’umma kuma ya zama kafar watsa labarai da mutane suka fi amfani da shi saboda saukin samunsa da sauransu.

An yi ittifaki cewa rediyo ne kafar watsa labarai da aka fi saurare duba da araha da saukin da yake da shi domin da kudi kadan mutum zai mallaki rediyo.

A wannan lokaci kuma rediyon ya koma a hannu domin da wayar hannu mutum zai iya sauraren rediyo.

Za a iya cewa yawaitar gidajen rediyo wani abu ne da ba a saba gani ba a yankin Arewa domin a yanzu haka gidajen rediyon da suke kan dogon zango na FM sun kai 40 a Jihar Kano.

Wasu daga cikinsu sun hada da Gidan Rediyon Kano da suke da tashoshin AM da FM, sai Pyramid da Freedom da Dala FM da Rahama da Arewa da Cool FM da Wazobiya da Express da Vision da Correct FM da Guarantee da Premier da Nasara da Jalla da S Radio da Liberty da sauransu.

Duk da cewa yawancin gidajen rediyon suna gabatar da shirye-shiryensu ne a harshen Hausa amma akwai wasu kadan da ke gudanar da shirye-shiryensu cikin harshen Ingilishi.

A duk yawan gidajen rediyon da ke jihar guda biyu ne rak suke karkashin gwamnati sauran kuma duk na ’yan kasuwa ne wadanda suka dogara da harkokin kasuwanci da suka shafi tallace-tallace wajen gudanar da gidajen rediyon.

Kamar yadda aka sani gidajen rediyo sukan gudanar da shirye- shirye a kullum kuma na tsawon yini guda.

Sai dai a yanzu daukar tsawon yini ana gudanar da shirye-shiryen ya zame wa akasarinsu wahala, maimakon haka wasu sukan gudanar da shirye-shiryen ne na wasu awanni duba da yanayin da kasar nan ta samu kanta a ciki na rashin tsayayyiyar wutar lantarki wadda ta janyo ake amfani da man dizel ko fetur wadanda farashinsu ya yi tashin gwaron zabo.

Wani abin da Aminiya ta lura da shi, shi ne ana samun wadannan gidajen rediyo suna maimaita shirye-shiryen juna.

Za a ga kusan duk shiryeshiryen da wannan gidan rediyo ke watsawa shi ne wancan gidan rediyon ke yi, sai dai bambancin sunan shirye-shiryen kawai.

Misali kusan dukkan gidajen rediyion babu wanda ba ya amfani da sojojin baka wajen yin shirinsa na siyasa.

A wasu lokutan ma idan kana sauraren wani shirin a wani gidan rediyon sai ka ji tamkar wanda ka gama saurara ne a wani gidan rediyon.

Har ila yau ana zargin irin wadannan gidajen rediyo da rashin biyan cikakken albashi ga ma’aikatansu ta yadda za a samu wasu gidajen rediyon ana daukar watanni kafin ma’aikaci ya samu albashi, yayin da wasu kuma suke biyan dan abin da bai taka kara ya karya ba, lamarin da ke jefa ma’aikatansu a harkar roko a duk lokacin da suka je daukar wani rahoto.

“Akwai gidan rediyon da kusan shekara bakwai da bude shi amma albashin da yake biyan ma’aikatansa tun wancan lokaci shi ne dai albashin da yake biya har yanzu wato Naira dubu 10,” in ji majiyarmu.

Wasu gidajen rediyon kuma suna dogara ne ga daliban manyan makarantu da ake kai musu don neman kwarewar aiki, idan an kai musu irin wadannan dalibai za a samu da sun gama karatunsu sai su rike su da sunan aiki kyauta kafin lokacin da za a dauke su aiki na dindindin.

“Su suna ganin kamar alfarma aka yi maka tunda an ba ka katin shaidar gidan rediyon to an ba ka kokon bararka,’’ in ji majiyar.

Bala Nasir dan jarida ne mai sharhi a kan al’ámuran yau da kullum ya ce yawaitar gidajen rediyo abu ne mai kyau sai dai akwai matsalolin da suka dabaibaye harkar.

Ya ce, “A ra’ayina gidajen rediyon da a yanzu haka ake budewa a Kano ba su yi yawa ba, domin idan kin duba a yanzu a Legas suna da gidajen rediyo kusan 100 kuma kowane aiki yake yi.

“Idan har zai zama cewa irin wadannan gidajen rediyo su zama suna fuskantar wata alkibla ta fuskar shirye shirye wannan babu laifi.

“Dama ce da Kundin Tsarin Mulki ya ba mutane, wanda duk yake da hali zai iya kafa gidan rediyo matukar ya cika sharuddan kafawa.

“Sai dai ya kamata ya zama kowane gidan rediyo yana da masu saurarensa.

“Kamar a nan Kano akwai gidan rediyon da abin da ya fi mayar da hankali a kansa shi ne noma.

“Haka akwai wanda sha’anin kasuwanci ya fi mayar da hankali a kai, duk da cewa mutane ba su fuskanci hakan ba, amma na san nan ba da dadewa ba za a gane hakan.”

Game da batun rashin kwararrun ma’aikata a irin wadannan gidajen rediyo, Bala Nasir ya cewa wannan abu babu musu a kai, domin hakan shi ya haifar da daukar shirye-shirye daga gidan wannan rediyo zuwa wancan duk da cewa akan dan samu bambancin suna shirin, amma idan ka natsu za a gane cewa duk manufar shirye shiryen iri daya ce.

Da zai zama cewa irin wadannan gidajen rediyon suna da kwararrun masu gudanar da su a samu shirye-shirye wadanda suke mabambanta da kuma ma’ana da sauransu.

Da a ce an samu kwararun ma’aikata a lokacin da aka bude kowane gidan rediyon sun zauna sun yi tunani tare da tsara masa shirye shiryensa na kashin kansa, to da watakila ba za a samu kwafe-kwafen shiryeshirye daga wani gidan rediyon zuwa wani ba.

Yawaitar gidajen rediyon ta janyo bude cibiyoyin koyar da aikin jarida barkatai a jihar wadanda suke ba kowa lasisi ko satifiket na zama dan jarida cikin kankanen lokaci.

A kan haka Bala Nasir ya ce “Wannan ba za a ce abu ne marar kyau ba, sai dai abin da za a sa ido a kai, shi ne ya zama cewa ana duba wadanda suke koyarwa a irin wadannan makarantu, shin kwartaru ne ko ’yan shan kai ne wadanda suke neman kudi?

“Wannan kuwa aikin hukuma ce inda za ta hada kai da kwararru daga makarantun gwamnati da suke koyar da wannan fanni don tantance tsaba daga tsakuwa.”

Ya bayyana cewa Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC) tana aiki, sai dai akwai kalubale na shari’a.

Ya ce, “Ita Hukumar NBC kasancewar doka ce ta kafa ta tana da iyakar huruminta wanda in ta tsalalke masu kafafen watsa labaran za su iya kai ta kotu su yi nasara kamar yadda ta faru ga wasu kafafen watsa labarai, inda suka yi karar hukumar a kan cin su tara da ta yi sakamakon wasu rahotanni da suka watsa da Hukumar NBC ke ganin sun saba ka’ida.

“A karshe dai kafofin watsa labaran ne suka yi nasara. Kin ga wannan ya zame wa hukumar takunkumi domin ba za ta iya hukunta gidajen rediyon ba sai dai ta kwabe su.”

Ya yi kira ga Hukumar NBC da Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) su yi aiki tukuru wajen tantance mutanen da ya kamata su yi aikin jarida duk da cewa a ’yan shekarun nan Kungiyar NUJ ta ce sai idan mutum yana da shaidar digiri zai yi aikin jarida.

Haka kuma akwai bukatar su tika yi wa ’yan jarida ko kafafaen watsa labarai linzami musamman ganin mafi yawan masu gidajen rediyon ba ’yan jarida ba ne.

Wani dan jarida Aminu Muhammad Gama ya ce yawan bude gidajen rediyon abu ne na gasar sana’a “Kin san mutane suna da wata dabi’a ko abu kake sayarwa da zarar an ga kana ciniki to in sha Allahu kowa zai dawo wannan harkar har sai an hadu an yi mata ragas ta mutu.

Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi shi ne Shugaban Sashen Nazarin Aikin Jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce yawaitar gidajen rediyo abu ne mai kyau matukar kafafen watsa labaran za su samar wa masu saurarensu abin da suke bukata.

“Idan kika dauke shi ta fuskar ilimi zai zama cewa an fadada dama ta samun labarai, sai dai kuma za ki ga akwai matsala ta fuskar rashin kwararrun ma’aikata wadanda ba su karanci aikin jarida ko darasssn da suke da dangantaka da aikin jarida ba.

“To akwai matsala haka kuma shi ma biyan albashin da bai taka kara ya karya ko kuma ma a wani wurin babu dungurugum, wannan ma matsala ce babba.

“Idan har ya kasance akwai karancin wadannan abubuwa to babu shakka ba za ka iya samar wa masu saurarenka abin da suke bukata ba.

“Yayin da ya zama ba ka iya biya wa masu saurarenka abin da suke so ba, to shi ke nan wata rana kana ji kana gani dole ka rufe domin ba zai yiwu ka ci gaba da zuba jarinka a harkar da kake yin asara ba,” in ji shi.