Tun bayan dawowa hutun dole na gasar Zakarun Turai, inda aka kwashe kusan wata biyar bayan an kammala wasannin farko na zagaye na biyu a gasar, sai gasar ta rika canja zani.
Yadda ta kaya a wasanni na biyu na zagaye na biyu
A wasannin na zagaye na biyu, wanda ake kira da Round of 16, an tafi hutun ne bayan an buga wasa daya. Don haka bayan an dawo wasa daya kawai aka buga.
Juventus da Lyon
Juventus ta doke kungiyar Lyon ta Faransa da ci biyu da daya a gidan Lyon din, wanda jimilla ya kama biyu da biyu kasancewar Lyon ta doke Juventus da ci daya da nema a gidan Juventus. Amma duba da Lyon ta doke Juventus a gidanta, sannan kuma ta samu kwallo daya a nata gidan, sai ta fitar da Juventus din.
Manchester City da Real Madrid
Manchester City ta doke Real Madrid ta ci biyu da daya, jimilla hudu da biyu bayan ta doke ta da ci biyu da daya a wasan farko. Hakan ya sa aka yi fitar da Real Madrid.
Liverpool da Atletico Madrid
Liverpool mai rike da kambun gasar ta sha kashi wajen kungiyar Atletico Madrid ne da ci uku da biyu, jimilla ya kama hudu da biyu.
Sauran wasannin, sun hada da Bayern Munich da Chelsea, inda Bayern din ta lallasa Chelsea da ci bakwai da daya a wasa biyu. Barcelon ta fitar da Napoli, sannan PSG ta fitar da Dortmund.
Wasannin ba-zata
A wasannin kusa da wasan kusa da karshe, wato Last 8, an yi wasannin masu dadi da zafi, amma tattare da mamaki da ba-zata.
Kasancewar Hukumar UEFA ta zo da sabon tsari na buga wasannin a waje daya, sannan wasa daya za a buga saboda kariya da cutar Covid-19, sai ya kasance kifa daya kwale ake yi.
PSG da Atalanta
A wasan da kusan kowa bai damu da shi ba, kasancewar ana tunanin PSG ta fi karfin Atlanta ta Italiya, da kyar PSG din ta sha.
Dan wasan Atlanta Mario Pašalić ne ya fara zura kwallo a ragar PSG a minti 26.
Daga nan aka ci gaba da tata-burza, har sai da aka kai minti 90 kafin dan wasan PSG Marquinhos ya farke musu.
Sannan a cikin karin minti biyar da aka yi wato a minti 93, dan wasan PSG Choupo-Moting ya kara jefa kwallo a ragar Atlanta.
RB Leipzig da Atletico Madrid
Kungiyar RB Leipzig wadda ta lallasa Tottenham, ita ma ana mata kallon kanwar lasa, amma cikin mamaki sai ta yi waje da kungiyar Atletico Madrid da ci biyu da daya.
Wannan wasan bai zo da abin mamaki ba sosai kasancewar za a iya cewa kungiyoyin biyu suna kusan mataki daya ne.
Amma wasan ya yi zafi matuka musamman duba da yadda Leipzig ta fara zura kwallo a minti 50, Atletico ta farke a minti 70, sannan Leipzig ta kara a minti 88.
Barcelona da Bayern Munich
A wasan da ya fi kowanne ba-zata, kungiyar Bayern Munich ce ta yi wa Barcelona dukan rabani da yaro, inda ta lallasa ta da ci 8 da 2.
Wasan ya ba masu kallon kwallon kafa da dama mamaki, musamman kasancewar ana ganin Barcelona ta fi karfin irin wannan wulakancin.
Manchester City da Lyon
A wani wasan da shi ma ya zo da ba-zata, shi ne yadda kungiyar Lyon ta doke Manchester City da ci 3 da 1.
Kasancewar an yi waje da Real Madrid da Juventus da Barcelona, sai ake ganin Man City ta samu damar lashe gasar, inda ake ganin ita ce kadai za ta iya fafatawa da Bayern Munich. Amma sai Lyon ta mata ba-zata.
Yau da gobe za a fafata wasan kusa da karshe
Yau ce za a fafata wasa tsakanin RB Leipzig da PSG a wasan farko na wasannin kusa da karshe.
Sannan gobe a fafata tsakanin Lyon da Bayern Munich.
Kungiyar da ta lashe wasan yau, da wadda ta lashe wasan gobe ne za su fafata a wasan karshe a ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta.
A yanzu dai kungiyar PSG da Bayern Munich ne manyan kungiyoyin da suka rage, kuma dukkansu suna neman kofin Zakarun Turai ruwa a jallo.
Ita PSG ba ta taba lashe gasar ba, ita kuma Bayern Munich tun shekarar 2013 rabon da ta sake lashewa.
Abin da ake jiran gani shi ne, shin bana gasar za ta yi ba-zata har karshe ne?
Idan kuwa ta yi hakan, masoya kwallon kafa suna tsammanin ganin Leipzig ko Lyon ta lashe kofin.
Ko kuma Bayern Munich da ta dade tana neman sake lashe kofin, ko kuma ita PSG din da ta dade tana kashe kudi wajen sayan manya ’yan wasa domin lashe gasar.