Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray a wannan Alhamis din ta sanar da daukar dan wasan Jamus, Leroy Sane daga Bayern Munich.
Kungiyar ta Turkiyya ta dauki dan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Munich.
- Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu
- Ƙwazo da juriya suka sa na zura ƙwallaye 10 a wasanni 10 – Mane
Sane mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru uku inda zai rika daukar albashin Yuro miliyan 9 — kwantankwacin Dala miliyan 10.4 — duk shekara kamar yadda kulob din bayyana.
A kakar bana Sane ya jefa kwallaye 13 a duk gasannin da ya haska, inda ya taimaka wa Bayern lashe gasar Bundesliga bayan ta subuce daga hannunta a kakar bara.
AFP