A ranar Talatar da ta gabata ce aka samu labarin cewa fitaccen dan wasan Kungiyar Real Madrid da kasar Jamus Toni Kroos zai yi ritaya daga buga kwallon kafa.
Dan wasan zai buga wasan karshe na Gasar Zakarun Turai, wanda za a fafata tsakanin Real Madrid da Kungiyar Dortmund ta kasar Jamus, sannan zai wakilci kasarsa ta Jamus a gasar Nahiyar Turai ta shekarar 2024 a matsayin wasannin karshe da zai taka leda.
Fitaccen dan jaridar kwallon kafa, Fabrizio Romano ne ya tabbatar da haka, inda ya sanar da cewa, “A ranar 17 ga Yulin shekarar 2014 ce aka gabatar da ni a matsayin sabon dan wasan Kungiyar Real Madrid, wanda ranar ce ta canja rayuwata a matsayin dan kwallo. Bayan shekara 10, na yanke shawarar daga wannan kakar, zan dakata haka.
- Ba ni da hannu a dawowar Aminu Ado Bayero Kano — Ribadu
- Shugabannin tsaro sun gana da Sanusi da Abba a fadar Sarkin Kano
“Ba zan taba mantawa da nasarorin da na samu a nan ba. Ina godiya ga duk wanda ke da alaka da wannan kungiya da taimakon da na samu har zuwa wannan mataki.
“Uwa-uba, ina godiya ga dimbin magoya bayan wannan kungiya, wadda ita ce ta daya a duniyar kwallon kafa bisa kaunar da suka nuna min daga farko da na zo, zuwa wannan lokaci.
“Ba wai Real Madrid kadai zan bari ba, kwallon kafa baki daya ne zai yi ritaya daga bugawa.
“Na dade ina da burin ganin na kammala buga kwallo ina cikin ganiyata.
“Ba na son in kai lokacin da zan fara zama a benci, don haka na yanke shawarar dakatawa a lokacin da kwallon ke yi da ni.
“Yanzu babban burina shi ne Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai karo na 15. Hala Madrid,” in ji Kroos.
Tarihin dan wasa Toni Kroos
An haifa Toni Kroos ne a ranar 4 ga Janairun 1990 a garin Greifswald da ke yankin Mecklenburg-Borpommern na kasar Jamus.
Mahaifinsa, Roland tsohon mai horar da matasan ’yan kwallo ne a Kungiyar Hansa Rostock.
Tun yana karamin ya kasance mai saukin kai, wanda abokansa a makaranta suke kauna da girmamawa.
Yana da mace mai suna Jessica Farber, wadda ya aura a ranar 13 ga Yunin shekarar 2015, kuma suna da ’ya’ya biyu mace da namiji.
Ya fara kwallon yarinta ne da Kungiyar Greifswald SC, sannan ya koma Kungiyar Hansa Rostock, sannan ya koma kungiyar kwallon kafa ta matasa ta Bayern Munich a shekarar 2016.
A kakar shekarar 2007-2008 lokacin yana dan shekara 17 Kroos ya fara taka leda a babbar Kungiyar Bayern Munich, inda ya fara taka leda a wasan da Bayern ta lallasa Energie Cottbus, inda ya taimaka wa tsohon dan wasan Jamus da Bayern Munich ya zura kwallo biyu a wasansa na farko a ranar 26 ga Satumban 2007 a cikin minti 18 da ya buga a wasan.
A Janairun shekarar 2009 Bayern Munich ta tura matashin dan wasan aro a Kungiyar Bayer Leverkusen na wata 18 domin ya kara gogewa, inda ya fara wasa a ranar 28 ga Fabrairun shekarar a wasan Leverkusen da Hannober 96.
A Kungiyar Real Madrid dan wasan ya fi tashe, inda ya lashe kofi 21 da sauran nasarori da dama.
Buga wa Jamus kwallo
Kusan za a iya cewa ’yan Nijeriya sun fara sanin dan wasan ne a Gasar Cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17 wanda aka buga a kasar Koriya ta Kudu, inda Nijeriya ta doke kasar Spain a wasan karshe a bugun finareti.
A gasar, kasar Jamus ce ta zo ta uku, inda Toni Kroos ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan gasar. Sai dan wasan Nijeriya, Crisantus Macauley ya lashe kambun wanda ya fi zura kwallaye a gasar da kwallo bakwai,
Ransford Osei na Ghana na zura kwallo shida, sannan Kroos ya zura kwallo biyar.
Tun daga lokacin ne Kroos ke ta samun ci gaba, har ya kai matakin da duniya ke jin sa, musamman bayan zuwansa Real Madrid.
Masu sharhi a kan wasanni, musamman a Nijeriya sukan ce duk da cewa a shekara daya suka fara fitowa, inda dan Nijeriya Macauley ya fi zura kwallo, sai Osei ke biye masa kafin Kroos, amma yanzu an daina jin duriyarsu baki daya sai Kroos.
Yanzu Ransford Osei ba ya da kungiya, inda karshe da aka samu labarinsa shi ne buga wa kungiyar Palanga ta kasar Lithuanian a shekarar 2019.
Tun lokacin ba a sake jin duriyarsa. Shi kuma Macauley na Nijeriya, an samu labarin ya buga wa Kungiyar Lynd FC a shekarar 2023, amma Aminiya ta ziyarci shafinta, inda ta ga babu sunan dan wasan a cikin ’yan wasanta na yanzu.
Kofunan da ya lashe
Bayern Munich
Bundesliga: 2007-2008, 2012- 2013, 2013-2014 DFB-Pokal: 2007-2008, 2012- 2013, 2013-2014 DFL-Supercup: 2012 Gasar Zakarun Turai: 2012-2013 UEFA Super Cup: 2013 FIFA Club World Cup: 2013
Real Madrid
La Liga: 2016-2017, 2019-1020, 2021-2022, 2023-2024 Copa del Rey: 2022-2023 Supercopa de España: 2017, 2019-2020, 2021-2022, 2023- 2024 Zakarun Turai: 2015-2016, 2016-2017, 2017-2018, 2021- 2022 UEFA Super Cup: 2014, 2017, 2022 FIFA Club World Cup: 2014, 2016, 2017, 2018, 2022
Jamus
Kofin Duniya: 2010 Nasarorin da ya samu
Tuni ’yan Real Madrid suka fara nuna alhininsu da wannan ba-zata da suke cewa dan wasan ya yi musu na yin ritaya a lokacin da suke kaunarsa.
Sai dai ya ce dama burinsa ke nan, ya yi ritaya a lokacin da yake ganiyarsa, ba sai an gaji da shi ba, wanda kuma hakan za a yi.