✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayern Munich ta naɗa Kompany sabon kociyanta

Bayern ta yi fadi tashi wajen neman kociyan da zai maye gurbin Tuchel.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayern Munich da ke Jamus ta ɗauki Vincent Kompany a matsayin sabon kociyanta.

Munich ta kulla yarjejeniya da Kompany ɗan kasar Belgium mai shekara 38 kan kwantaragin kaka uku.

Kompany ya maye gurbin Thomas Tuchel, wanda ya bar Bayern Munich a watan nan, bayan da kungiyar ta kare a mataki na uku a teburin Bundesliga — mataki mafi muni tun bayan 2010/11.

Bayern ta yi fadi tashi wajen neman kociyan da zai maye gurbin Tuchel, wanda tun cikin watan Fabrairu ya sanar da zai bar ƙungiyar.

Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso da na tawagar Jamus, Julian Nagelsmann da na Austria, Ralf Rangnick, duk ba su yadda sun karɓi ragamar horar da Bayern Munich ba.

Bayern Munich ta yi kokarin ta rarrashi Tuchel ya ci gaba da horar da ita, daga baya batun ya ci karo da cikas.

Sabon kociya Kompany shi ne ya lashe Championship da Burnley a 2022-23, amma ƙungiyar ta kasa ci gaba da gwagwarmaya a Firimiyar Ingila a bana, bayan da ta ƙare ta 19 a kasan teburi, inda ta sake komawa gidan jiya.

Kompany, wanda ya yi ritaya daga taka leda a 2020, ya karɓi aikin horar da Burnley daga Anderlecht a 2022, wanda ya tsawaita yarjejeniyarsa a bara zuwa kaka biyar.